EndSARS: Dan Najeriya ya maka Twitter a kotu, ya bukaci diyyar $1bn

EndSARS: Dan Najeriya ya maka Twitter a kotu, ya bukaci diyyar $1bn

- Adamu Garba, dan kasuwa a Najeriya ya maka shugaban kamfanin Twitter, Jack Dorsey a kotu

- Kamar yadda karar ta nuna, Garba yana zargin Jack Dorsey da daukar nauyin zanga-zangar EndSARS

- Amma kuma Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ta tabbatar da cewa har yanzu ba a bai wa karar alkali ba

Wani dan kasuwar Najeriya, Adamu Garba, a ranar Talata ya maka shugaban kamfani kuma mamallakin Twitter, Jack Dorsey, a gaban wata kotun tarayya da ke Abuja.

Hakan ta faru ne bayan da ya zargi shugaban kamfanin Twitter da daukar nauyin zanga-zangar EndSARS a fadin kasar nan, Vanguard ta wallafa.

A kararsa mai lamba FHC/ABJ/CS/1391/2020 wacce lauyansa, Abbas Ajiya ya shigar, ya bukaci kotun da ta umarci Dorsey da ya tsayar da al'amuran kamfaninsa a dukkan sassan kasar nan.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya sanar da cewa har yanzu ba a bai wa karar alkali ba.

Daga cikin masu kare kansu akwai ministan shari'a na Najeriya, mai bada shawara a fannin tsaron kasa, Sifeta janar na 'yan sanda, darakta janar na hukumar tsaro ta farin kaya, shugaban soji, shugaban NSCDC, Jack Dorsey da kuma masu zanga-zangar.

A bukatar Adamu Garba, ya bukaci kotun da ta biya shi dala biliyan daya a matsayin diyya.

KU KARANTA: Budurwa ta yagalgala wa saurayi takardun shaidar karatun sa bayan sun yi fada (Hotuna)

EndSARS: Dan Najeriya ya maka Twitter a kotu, ya bukaci diyyar $1bn
EndSARS: Dan Najeriya ya maka Twitter a kotu, ya bukaci diyyar $1bn. Hoto daga @AdamuGarba, @Jack
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon matashi mai digiri na biyu da shaidun makaranta 30 yana tallar kwai

A wani labari na daban, wasu fusatattun matasa a garin Ibadan da ke jihar Oyo, sun banka wa ofishin 'yan sanda da ke Ojoo wuta. Ganau ba jiyau ba sun sanar da The Cable cewa rikicin ya fara ne bayan 'yan sanda sun yi yunkurin watsa masu zanga-zanga.

Wasu da ake zargin 'yan daba ne a cikin gayyar masu zanga-zangar sun dinga jifan 'yan sandan da duwatsu wanda hakan yasa 'yan sandan suka bude wuta.

Fusatattun masu zanga-zangar sun fi 'yan sandan yawa kuma sun shige cikin ofishin inda suka banka masa wuta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel