Bidiyon matashi mai digiri na biyu da shaidun makaranta 30 yana tallar kwai

Bidiyon matashi mai digiri na biyu da shaidun makaranta 30 yana tallar kwai

- Wani saurayi mai suna Dennis Obilo, bayan kammala digirinsa na biyu, rashin aikin yi yasa ya koma sayar da kwai akan titi

- Saurayin mazaunin Nairobi ya sha wahalhalun rayuwa kafin ya kammala karatukansa amma duk da haka bai samu aiki ba

- Obilo yana da takardu na makarantu da jami'o'i daban-daban wanda ya karanta fannoni iri-iri na ilimi kusan guda 30

Wani saurayi mazaunin Nairobi, bayan kammala digirinsa na biyu, ya koma sayar da kwai a bakin titi sakamakon rashin samun aiki.

Dennis Obilo, wanda ya kammala difuloma, digiri, da kwalaye fiye da 30 wadanda duk ya samu a makarantu da jami'o'in dake kasar ya koma sayar da kwai, yanzu haka yana digirinsa na biyu ta yanar gizo.

Iyayen Obilo talakawa ne tilis, ya kuma taso a Rongo, Legit.ng ta wallafa.

Tun yana karami yake fafutukar neman na tuwo, al'amarin ya munana bayan rasuwar mahaifinsa a lokacin yana da karancin shekaru.

Wahalhalun taso da shi da kanninsa 5 sun koma kan mahaifiyarsa wadda bata da aikin yi in banda wata 'yar karamar gonar da take nomawa.

KU KARANTA: Bidiyon ragargazar 'yan Boko Haram da sojin sama suka yi a maboyarsu a Borno

Bidiyon matashi mai digiri na biyu da shaidun makaranta 30 yana tallar kwai
Bidiyon matashi mai digiri na biyu da shaidun makaranta 30 yana tallar kwai. Hoto daga Dennis Obilo
Asali: UGC

Sai bayan makwabcinsu ya lura da yadda Obilo ke son karatu ya dauki nauyinsa tare da yaransa.

Dr Charles Mulli ya hada Obilo da yaransa inda ya cigaba da daukar dawainiyar karatunsa.

Obilo ya cigaba da mayar da hankalinsa akan karatu, inda ya kammala firamare a 2003. Ya kammala sakandire 2007, inda yake cikin masu hazakar ajinsu, a lokacin yana da shekaru 18 da haihuwa.

Makwabcin nasu ya cigaba da daukar nauyin karatunsa bayan ganin hazakarsa.

Inda ya kammala jami'a a 2010, ya cigaba da karatuttuka na jami'a iri har 2018. Yanzu haka kwalayensa 30 na karatuttuka daban-daban da yayi, amma babu aikin yi.

KU KARANTA: Zargin damfara: Kotu ta bai wa Sanata Ndume kwana 21 ya kawo Maina

KU KARANTA: Gwamnati bata da karfin samar wa da jama'a isassun ayyukan yi - Ngige

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace matasa su na da hakkin yin zanga-zanga don sanar da shugabanninsu matsalarsu, Vanguard ta ruwaito.

Ya ce yakamata a ba wa matasa damar bayyanar da damuwarsu da hakkinsu ga gwamnati, amma kada su bar 'yan ta'adda da bata-gari su shiga harkar.

Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, ya sanar da hakan bayan taron da yayi da shugaban kasa a fadarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel