Budurwa ta yagalgala wa saurayi takardun shaidar karatun sa bayan sun yi fada (Hotuna)

Budurwa ta yagalgala wa saurayi takardun shaidar karatun sa bayan sun yi fada (Hotuna)

- Ashe makashinka yana nan tare da kai, amma wasu basu gane ba. Wata budurwa tayi kaca-kaca da takardun makarantar saurayinta

- Saurayin mai amfani da su na @somambia, ya wallafa yadda budurwarsa ta yaga masa duk takardunsa a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter

- Somambia ya shawarci maza da su san irin matan da za su dinga mu'amala da su, don a kwanakin baya al'amarin ya faru, amma har yanzu yana jin radadi a ransa

Wani saurayi ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, mai suna @somambia ya bayyana yadda tsohuwar budurwarsa ta yayyaga duk kwalayensa na makaranta a kwanakin baya.

A yadda ya wallafa, har yanzu al'amarin na damunsa, ya shawarci 'yan uwansa maza da su san irin matan da za su dinga mu'amala dasu.

Somambia yace takardun da tsohuwar budurwarsa ta yaga masa sun hada da takardunsa na makaranta, na haihuwa da kuma takardun aikinsa na kamfani.

A cewarsa, yana tuna ranar da ta yaga masa takardunsa har yanzu.

Ga yadda ya wallafa: "Bazan taba manta ranar nan ba, kamar jiya al'amarin ya faru. Ka tabbatar ka samu mace mai hankali idan za ka yi soyayya."

Sauran masu amfani da kafar sada zumuntar zamanin, sun yi ta nuna masa tausayi da kuma mamakin yadda budurwar da mutum ke so za ta aikata masa wannan mummunan aikin.

Wani @oneko cewa yayi: "Ashe makashinka yana nan tare da kai, da fatan duk zamu fahimci hakan."

Wani @ookumusteve cewa yayi: "Ina fatan makarantun da kayi za su kara baka wasu takardun, nima na taba batar da nawa takardun, nasha wahala."

KU KARANTA: EndSARS: Kuna da hakkin yin zanga-zanga - Buhari ya sanar da matasa

Budurwa ta yagalgala wa saurayi takardun shaidar karatun saurayi bayan sun yi fada
Budurwa ta yagalgala wa saurayi takardun shaidar karatun saurayi bayan sun yi fada. Hoto daga @somambia
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zargin damfara: Kotu ta bai wa Sanata Ndume kwana 21 ya kawo Maina

A wani labari na daban, an dakatar da dalibai 20 'yan aji 4 da ke babbar makarantar sakandire ta Loreto a Zimbabwe sakamakon kamasu da laifin lalata da juna a watan Yuli.

Da yake makarantar ta maza da mata ce, an kama daliban tsirara suna lalata a inda yara matan ke kwana na makarantar da ke Silobela, yayin da suke shirin fara jarabawar watan Yuni zuwa Yuli.

Kamar yadda rahoton yazo, "Mun samu labarin yadda aka kama daliban babbar makarantar Loreto da aka dakatar saboda kama su da aka yi suna lalata, duk da ba'a kamasu turmi da tabarya ba.

"Wasu iyayen daliban sun yi ta kiran waya suna rokon ma'aikatar ilimi da ta saka baki akan tsawon lokacin da aka dakatar da daliban. Don haka muka tura masu bincike a ranar Juma'a don jin tabbacin al'amarin. Yanzu haka muna jiran rahoto ne daga wurin su."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel