Da zafinsa: DSS ta gayyaci wani babban malamin addinin Kirista kan rikicin Jos

Da zafinsa: DSS ta gayyaci wani babban malamin addinin Kirista kan rikicin Jos

- Rundunar tsaron farin kaya DSS ta gayyaci wani babban malamin addinin Kirista mazaunin Filato, Isa El-Buba

- Rahotanni sun bayyana cewa gayyatar da DSS ta yiwa El-Buba ba zai rasa nasaba da zanga zangar #EndSARS da matasa suka gudanar a Jos ba

- A yayin zanga zangar ne da suka gudanar ranar Lahadi, El-Buba ya dage kan lallai Nigeria na hannun gurbatattun shuwagabanni, akwai bukatar canja su

Rundunar tsaron farin kaya DSS ta gayyaci wani babban malamin addinin Kirista mazaunin Filato, Isa El-Buba, da ya gurfana a ofishinta na Jos a ranar Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa gayyatar El-Buba, wanda shine shugaban cocin Evangelical Bible Outreach Ministries, ba zai rasa nasaba da zanga zangar #EndSARS a garin Jos ba.

A ranar Lahadin da ta gabata, shi El-Buba ya jagorancin addu'a yayin tafiya, wacce masu zanga zangar #EndSARS suka shirya a garin Jos, jihar Filato.

KARANTA WANNAN: AGF ya amince a sallami jami'an SARS 35, kuma a yi masu hukunci

Da zafinsa: DSS ta gayyaci wani babban malamin addinin Kirista kan rikicin Jos
Da zafinsa: DSS ta gayyaci wani babban malamin addinin Kirista kan rikicin Jos - The Guardian Nigeria / Vanguard News
Asali: UGC

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa addu'a yayin tafiyar ya gudana ne daga shatale talen tshohuwar tashar jirgin sama zuwa babbar sakatariyar jihar.

KARANTA WANNAN: An aika takardar korafi a kan Buhari zuwa UK da USA saboda nadin wani mukami

Dandazon mutane ne suka halarci wannan zanga zanga musamman matasa, inda shi malamin addinin Kiristan ya dage kan lallai Nigeria na hannun gurbatattun shuwagabanni.

Wani mamba na cocin, wanda ya bukaci The Punch ta sakaya sunansa ya tabbatar da cewa hukumar DSS ta gayyaci El-Buba a ranar Talata a Jos.

Wata majiya ta bayyana cewa DSS ta bukaci El-Buba ya gurfana a ofishinta na Jos a ranar Talata. Kuma har yanzu basu sake shi ba, tun bayar isarsa ofishin da misalin karfe 10 na safe.

A wani labarin, Ministan matasa da bunkasa rayuwa, Sunday Dare a ranar Litinin ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari, dangane da zanga zangar da ake ci gaba da yi ta kawo karshen SARS.

Bayan kammala ganawar, Ministan ya shaidawa manema labarai cewa shugaban kasa Buhari ya shaida masa cewa ba shi da ta cewa kan matasan da ke zanga zanga.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel