Babbar magana: AGF ya amince a sallami jami'an SARS 35, kuma a yi masu hukunci

Babbar magana: AGF ya amince a sallami jami'an SARS 35, kuma a yi masu hukunci

- Abubakar Malami (SAN) ya sanya hannu kan bukatar da hukumar NHRC ta gabatar masa na sallamar jami'an SARS 35 daga aikin dan sanda

- An ciro sunayen jami'an rusasshiyar rundunar SARS daga jihohi 12 da kuma babban birnin tarayya Abuja bayan gudanar da bincike a kan su

- Laifukan da jami'an suka aikata da ya sa aka sallame su sun hada da kisan farar hula, garkame mutane ba bisa ka'ida ba, cin zarafi da dai sauransu

Antoni Janar na kasa kuma ministan shari'a, Abubakar Malami (SAN) ya karbi sunayen jami'an rusasshiyar rundunar SARS guda 35 domin a sallamesu daga aikin dan sanda.

KARANTA WANNAN: Sabbin mutane 118 sun kamu da cutar COVID-19, mutane 1125 sun mutu

Sakataren hukumar kare hakkin bil Adama ta kasa (NHRC), Tony Ojukwu a ranar Litinin ya gabatar wa AGF sunayen jami'a 35 da suka fito daga jihohi 12 da babban birnin tarayya Abuja.

Da ya ke zantawa da manema labarai, Ojukwu ya ce jami'an da aka sallama an same su da laifukan kisa ba gaira babu dalili, cafkewa da tsarewa ba tare da izini ba, da cin zarafi.

Babbar magana: AGF ya amince a sallami jami'an SARS 35, kuma a yi masu hukunci
Babbar magana: AGF ya amince a sallami jami'an SARS 35, kuma a yi masu hukunci - @daily_trust
Asali: Twitter

Sauran laifukan da suka aikata sun hada da kwace kaya da garkame asusun fararen hular da ba su ji ba basu gani ba, da sauran laifukan da suka aikata a yayin da su ke bakin aiki.

Bukatar da hukumar NHRC ta gabatar wa ofishin AGF na sallamar jami'an 35 na tare da wasu manyan takardu da ke dauke da hujjojin zarge zargen da ake yi musu bayan gudanar da bincike.

KARANTA WANNAN: Muhimmin sakon shugaba Buhari ga masu zanga zanga - Ministan Matasa

A wani labarin, Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi a ranar Litinin ya ce gwamnatin jihar ba za ta lamunci kai cin zarafin da jami'an 'yan sanda ke yiwa al'umar jihar ba.

Mr Umahi, wanda ya bayyana hakan a babban dakin taro na tsohon gidan gwamnatin jihar yayin ganawa da masu zanga zangar #EndSARS, ya ce ba zai lamunce tsare tituna a ko ina a jihar ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel