Na haramtawa 'yan sanda sanya shingen bincike a titunan jiha ta - Gwamna Umahi

Na haramtawa 'yan sanda sanya shingen bincike a titunan jiha ta - Gwamna Umahi

- Gwamnatin jihar Ebonyi ta ce ba za ta lamunci cin zarafi, kisan ba gaira babu dalili da tauye hakkin bil Adama da jami'an 'yan sandawa ke yiwa jama'a ba

- Gwamna Umahi na jihar, ya ce ya haramtawa rundunar 'yan sanda sanya shingen bincike a tintunan da ke cikin jihar

- Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Litinin a babban dakin taro na tsohon gidan gwamnatin jihar yayin ganawa da masu zanga zangar #EndSARS

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi a ranar Litinin ya ce gwamnatin jihar ba za ta lamunci kai cin zarafin da jami'an 'yan sanda ke yiwa al'umar jihar ba.

Mr Umahi, wanda ya bayyana hakan a babban dakin taro na tsohon gidan gwamnatin jihar yayin ganawa da masu zanga zangar #EndSARS, ya ce ba zai lamunce tsare tituna a ko ina a jihar ba.

DUBA WANNAN: Rundunar soji za ta fara atisayen murmushin kada a fadin Nigeria

Gwamnan ya ce zai gana da kwamishinan 'yan sanda da kuma kwamandan rundunar sojin jihar don tabbatar da bin wannan umurni cikin gaggawa.

Jaridar Premium Times ta ruwaito Umahi na cewa "Zamu lamunci jami'an tsaro su tsaya a gefen titi, su tsare tare da bincikar duk wata mota da za ta wuce tare da fasinjojin cikin ta.

Ba zan lamunci tashe tashen hankulan masu zanga zanga a jiha ta ba - Gwamna Umahi
Ba zan lamunci tashe tashen hankulan masu zanga zanga a jiha ta ba - Gwamna Umahi - Vanguard Newspaper & The Eagle Online
Asali: UGC

"Ku nuna turjiyarku ga duk wani jami'in tsaron da ya tsare ku tare da tambayar ku na goro, ya isa haka nan," a cewar sa.

Ya bukaci masu zanga zangar da su kasance masu nuna dattako tare da gudanar da zanga zangar cikin lumana yana mai cewa, yin hakan ne zai sama masu mafita kan abunda su ke nema.

KARANTA WANNAN: An aika takardar korafi a kan Buhari zuwa UK da USA saboda nadin wani mukami

"A ranar Talata za mu kafa kotun bincike kan cin zarafin da jami'an 'yan sanda su ke yiwa jama'a, da kuma kisan ba gaira babu dalili, tare da karya hakkokin bil'Adama.

"Kotun za ta zamo karkashin alkalin babbar kotun shari'a, kuma za a sanya wakilan masu zanga zangar, kungiyoyin matasa, dalibai, kare hakkin bil'Adama da dai sauransu," a cewar sa.

A wani labarin, Ministan matasa da bunkasa rayuwa, Sunday Dare a ranar Litinin ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari, dangane da zanga zangar da ake ci gaba da yi ta kawo karshen SARS.

Bayan kammala ganawar, Ministan ya shaidawa manema labarai cewa shugaban kasa Buhari ya shaida masa cewa ba shi da ta cewa kan matasan da ke zanga zanga.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel