Gwamnati bata da karfin samar wa da jama'a isassun ayyukan yi - Ngige

Gwamnati bata da karfin samar wa da jama'a isassun ayyukan yi - Ngige

- Ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige, yace gwamnatin bata da damar samarwa matasa masu yawo cikin gari ayyukan yi, a wani taro da suka yi a Abuja ranar Litinin

- Ya roki ma'aikatu masu zaman kansu da su taimaka su samar da guraben da marasa ayyukan yi za su rabe don magance matsalar rashin aikin yi a kasar nan

- Ministan wanda ya samu wakilcin mataimakin jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar, ya nemi shawarwarin mutanen da suka je taron, don sanin yadda za'a bullowa al'amarin

Ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige, yace gwamnati bata da halin samarwa matasa marasa ayyukan yi da suke yawo kwararo-kwararo a titi ayyukan gwamnati, Daily Trust ta ruwaito.

Ngige ya roki ma'aikatu masu zaman kansu da su taimaka su samar wa marasa ayyukan yi wuraren da zasu rabe don kawo karshen rashin ayyuka a kasar nan.

A cewar ministan, kamar yadda takardar ta jami'in hulda da jama'a ya gabatar tace a Abuja a ranar Monday, yayin bude taron samar da ayyuka mai taken : "Samar da cigaban ma'aikatu masu zaman kansu".

Sakataren ma'aikatar, Yerima Peter Tarfa ne ya wakilci ministan, ministan ya ce aikin gwamnati kawai samar da wurare don taimakon ma'aikatu masu zaman kansu su samar wa marasa aiki gurbi.

Ministan ya nemi jin ta bakin wadanda suka je taron don samun shawarwari akan yadda za'a bullo wa lamarin.

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya kori shugaban hukumar hakkin mallaka

Gwamnati bata da karfin samar wa da jama'a isassun ayyukan yi - Ngige
Gwamnati bata da karfin samar wa da jama'a isassun ayyukan yi - Ngige. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Facebook

KU KARANTA: Zargin damfara: Kotu ta bai wa Sanata Ndume kwana 21 ya kawo Maina

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace matasa su na da hakkin yin zanga-zanga don sanar da shugabanninsu matsalarsu, Vanguard ta ruwaito.

Ya ce yakamata a ba wa matasa damar bayyanar da damuwarsu da hakkinsu ga gwamnati, amma kada su bar 'yan ta'adda da bata-gari su shiga harkar.

Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, ya sanar da hakan bayan taron da yayi da shugaban kasa a fadarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel