EndSARS: Kuna da hakkin yin zanga-zanga - Buhari ya sanar da matasa

EndSARS: Kuna da hakkin yin zanga-zanga - Buhari ya sanar da matasa

- Matasa suna da damar yin zanga-zangar lumana idan har wani al'amari ya damesu, domin hakkinsu ne yin hakan, inji shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Bayan wani taro da Ministan matasa da wasanni yayi da shugaban kasa, ya sanar da manema labaran cikin gidan gwamnati hakan

- Yace Buhari ya yaba da jajircewar matasan, amma ya shawarcesu da yin zanga-zangar lumana, kada su bar 'yan ta'adda su shiga lamarin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace matasa su na da hakkin yin zanga-zanga don sanar da shugabanninsu matsalarsu, Vanguard ta ruwaito.

Ya ce yakamata a ba wa matasa damar bayyanar da damuwarsu da hakkinsu ga gwamnati, amma kada su bar 'yan ta'adda da bata-gari su shiga harkar.

Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, ya sanar da hakan bayan taron da yayi da shugaban kasa a fadarsa.

Dare ya sanar da manema labaran cikin gidan gwamnati, cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki masu zanga-zangar da su dakata na wani lokaci don ba wa gwamnati dama, don yanzu haka an fara magance matsalar su.

Yace ya sanar da shugaban kasa zanga-zangar da matasa ke yi akan zalunci da cin zarafin da 'yan sanda ke yi wa al'umma.

A cewarsa, "Shugaban kasa yace ya ji korafi da koken da matasa ke yi, kuma yanzu haka yayi alkawarin kawo gyara a al'amarin."

Ya kara da cewa, "Ya yi matukar farin ciki da irin zanga-zangar lumana da aka yi don kawo korafi akan SARS, don haka shugaban kasa matsayin Uba yake ga matasa, zai tabbatar cewa ya kwatar musu hakkinsu.

"Matasa su na da damar yin zanga-zangar lumana idan wata matsala ta samesu, don tabbatar da gwamnati ta sa baki."

KU KARANTA: Dumu-dumu: Hukumar makaranta ta kama 'yan aji 4 na sakandare suna lalata a kungiyance

EndSARS: Kuna da hakkin yin zanga-zanga - Buhari ya sanar da matasa
EndSARS: Kuna da hakkin yin zanga-zanga - Buhari ya sanar da matasa. Hoto daga @Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Duba gagarumar motar da Ronaldo ya roka daga wurin fitaccen dan dambe Mayweather

A wani labari na daban, fitacciyar kungiyar malaman jami'o'i ta ce har yanzu tana nan a kan bakanta, bata dakatar da yajin aikinta ba.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa, shugaban kungiyar malaman reshen jihar Legas, Farfesa Olusiji Sowande, ya bayyana hakan a ranar Asabar, 17 ga watan Oktoban 2020.

Legeit.ng ta gano cewa, Sowande ya ce rahotannin kafafen yada labarai da ke ikirarin sun dakatar da yajin aikin ba gaskiya bane.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel