Duba gagarumar motar da Ronaldo ya roka daga wurin fitaccen dan dambe Mayweather

Duba gagarumar motar da Ronaldo ya roka daga wurin fitaccen dan dambe Mayweather

- Cikin wasa, gawurtaccen dan wasan kwallon kafa mai suna Cristiano Ronaldo, ya roki wani dan wasan damben mota

- Floyd Mayweather wani babban dan dambe ne a Amerika, wanda ya daina wasan dambe amma kuma yana da arziki mai tarin yawa

- Mayweather ya wallafa hotunan motocinsa a shafinsa na Instagram a daren Juma'a, inda cikin wasa Ronaldo ya rokesa motarsa kirar Bugatti

Cristiano Rinaldo wanda yanzu haka yake aiki da kungiyar wasan kwallon kafa ta Juventus dake Italiya, cikin wasa ya roki wani dan dambe Floyd Mayweather dan Amerika wata motarsa kirar Bugatti.

Floyd Mayweather na daya daga cikin 'yan wasa masu arzikin gaske duk da ya daina dambe yanzu haka.

Tun bayan barin harkar dambe, 'yan Amurka ke ta rokonsa akan ya dawo ya cigaba da harkar, amma yaki komawa duk da bai sanar wa duniya niyyarsa ba.

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya kori shugaban hukumar hakkin mallaka

Ubangiji ya azurta shi da dukiya mai yawa, inda yake da gidaje na gani da fadi a Amurka da sauran wurare na duniya, yana da motocin da yake hawa da na yaransa.

Baya ga wadannan, yana da jirgin sama, na kansa, wanda ke kai shi duk inda yake so a duniya.

Dan shekara 43 ya wallafa hotunan motocinsa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram, inda yake neman mabiyansa su zaba masa motar da zai fita da ita a daren Juma'a.

KU KARANTA: Operation Murmushin Kada: 'Yan Najeriya sun yi martani a kan sabon atisaye

Cristiano Ronaldo kuwa bai yi kasa a guiwa ba cikin wasa ya roki Mayweather da ya bashi kyautar Bugatti a cikin dumbin motocinsa. Duk da Ronaldo na cikin 'yan kwallon kafa masu arziki a duniya.

Duba gagarumar motar da Ronaldo ya roka daga wurin fitaccen dan dambe Mayweather
Duba gagarumar motar da Ronaldo ya roka daga wurin fitaccen dan dambe Mayweather. Hoto daga Daniele Badolato
Asali: Getty Images

Duba gagarumar motar da Ronaldo ya roka daga wurin fitaccen dan dambe Mayweather
Duba gagarumar motar da Ronaldo ya roka daga wurin fitaccen dan dambe Mayweather
Asali: Instagram

A wani labari na daban, Neymar yana daya daga cikin fitattun 'yan kwallon kafa da ke da aji da kuma salo. Yana da matukar arziki kuma har yau yana daya daga cikin 'yan kwallon kafa masu tsada a duniya.

A 2018, an gano cewa fitaccen dan kwallon yana da kudi da suka kai dala miliyan 185 kuma duk da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi sun fi shi kudi, za a iya cewa ya fi su yarinta.

A halin yanzu, kwagilarsa da kungiyar kwallon kafa ta Faransa tana samar masa da naira miliyan 298 a kowanne mako.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel