Neymar: Dan wasan kwallon kafan da ya mallaki motoci na N2bn (Hotuna da Bidiyo)
- Neymar na cigaba da kashe makuden kudade wurin siyan jiragen sama, na ruwa da kuma motoci
- Dan wasan kwallon kafar yana da gagarumin garejin mai dauke da jerin motocin da suka kai N2 biliyan
- Daya daga cikin motocinsa masu tsada akwai ta naira biliyan 7 kirar Koenigsegg CCXR
Neymar yana daya daga cikin fitattun 'yan kwallon kafa da ke da aji da kuma salo. Yana da matukar arziki kuma har yau yana daya daga cikin 'yan kwallon kafa masu tsada a duniya.
A 2018, an gano cewa fitaccen dan kwallon yana da kudi da suka kai dala miliyan 185 kuma duk da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi sun fi shi kudi, za a iya cewa ya fi su yarinta.
A halin yanzu, kwagilarsa da kungiyar kwallon kafa ta Faransa tana samar masa da naira miliyan 298 a kowanne mako.
Ya kware wurin kashe kudinsa a kan ababen more rayuwa. Ya mallaki jiragen sama biyu, jirgin ruwa daya wanda a kowacce shekara ake kashewa dala 120,000.
Ga jerin motocin da dan kwallon kafar ya mallaka.
KU KARANTA: Dumu-dumu: Hukumar makaranta ta kama 'yan aji 4 na sakandare suna lalata a kungiyance

Asali: Getty Images
• Mercedes AMG - N57.3 million
• Audi R8 Spyder - N59 million
• Maserati Mc12 - N245 million
• Volkswagen Touareg V8 FSI - N18 million
• Volvo XC 60 - N27.3 million
• Audi Q5 - N16 million
• Audi RS7 Sportback - N60 million
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan daba sun kaiwa tawagar gwamnan APC hari (Hotuna da bidiyo)
A wani labari na daban, wani mawaki mai suna Amzat Ibrahim, a ranar Alhamis ya sanar da wata kotun gargajiya da ke zama a Ile-Tuntun a Ibadan cewa matarsa fasika ce.
Ya sanar da yadda matarsa mai suna Zainab take lalata da babban amininsa. Amzat ya bayyana wannan zargin ne bayan Zainab ta sanar da kotun cewa yana farautar rayuwarta domin haka take so a raba aurensu.
"Mai shari'a, a gaskiya ni da Zainab muna fada ne saboda halin bin mazanta. Zainab da babban abokina suna fasikanci.
“Ta yi batan dabo na tswon watanni uku inda ta bar gidana. Ta kwashe yarana amma daga bisani sai na gano tana gidan abokina ne kuma amini.
"Dumu-dumu na kama su suna faskancin," Amzat yace.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng