Operation Murmushin Kada: 'Yan Najeriya sun yi martani a kan sabon atisaye

Operation Murmushin Kada: 'Yan Najeriya sun yi martani a kan sabon atisaye

- Za'a fara bibiyar labaran bogi da kuma kamo masu yada shi daga ranar Talata mai zuwa inji Kakakin rundunar sojin Najeriya, Musa Sagir

- Sagir ya fadi hakan ne bayan Zanga-zangar da matasa suka yi ta yi a 'yan kwanakin musamman a kafafen sada zumuntar zamani

- Yace ta kafafen ne kowa yake da damar baje kolinsa, har da masu zargin sojoji da kai musu farmaki yayin zanga-zangar

Kakakin rundunar sojin Najeriya, Musa Sagir yace za'a fara kaddamar da shirin ganowa da kuma kamo masu watsa labaran bogi a kafafen sada zumuntar zamani.

Al'amarin yazo ne bayan Zanga-zangar da 'yan Najeriya suke yi a biranen jihohi.

Yawancin zanga-zangar ana yin ta ne a kafafen sada zumuntar zamani, wanda har wasu daga cikin matasan masu zanga-zangar suke zargin sojoji da kai musu farmaki.

Wannan lamarin ya janyo cece-kuce daga jama'a inda suke fatan wannan sabon atisayen Murmushin Kada ya kasance alheri ba hanyar durkusar da matasa ba.

Ga wasu daga cikin tsokacin jama'a a kan sabuwar atisayen murmushin kadan:

KU KARANTA: Matar aure ta gurfana gaban kotu bayan ta soka wa makwabciya wuka a kai

Operation Murmushin Kada: 'Yan Najeriya sun yi martani a kan sabon atisaye
Operation Murmushin Kada: 'Yan Najeriya sun yi martani a kan sabon atisaye. Hoto daga @Thecable
Asali: Twitter

KU KARANTA: FG da gwamnonin arewa maso yamma sun hada kai wurin kawo karshen 'yan bindiga

A wani labari na daban, rikici ya barke a fitaccen wurin nan na shataletalen Ola-Iya da ke Osogbo, babban birnin jihar Osun yayin da wasu 'yan daba suka kai wa tawagar Gwamna Gboyega Oyetola hari.

'Yan daban sun jefe tawagar gwamnan da duwatsu, adduna tare da sanduna bayan ya kammala jawabi ga masu zanga-zangar EndSARS a babban birnin jihar.

Gwamnan ya yi tattaki tare da wasu 'yan majalisar jihar daga yankin Alekuwodo zuwa inda masu zanga-zangar suke a Ola-Iya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel