Da duminsa: ASUU ta bayyana matsayarta a kan yajin aiki

Da duminsa: ASUU ta bayyana matsayarta a kan yajin aiki

- Kungiyar malamai masu koyarwa na Jami'o'i, ta ce har yanzu bata dakatar da yajin aikinta ba

- Babba a kungiyar, Farfesa Olusiji Sowande, ya ce suna cigaba da tattaunawa da gwamnatin tarayya

- Sowande ya kara da cewa gwamnatin tarayya bata sakar wa malaman alawus dinsu ba akasin yadda rade-radi ke yawo a gari

Fitacciyar kungiyar malaman jami'o'i ta ce har yanzu tana nan a kan bakanta, bata dakatar da yajin aikinta ba.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa, shugaban kungiyar malaman reshen jihar Legas, Farfesa Olusiji Sowande, ya bayyana hakan a ranar Asabar, 17 ga watan Oktoban 2020.

Legeit.ng ta gano cewa, Sowande ya ce rahotannin kafafen yada labarai da ke ikirarin sun dakatar da yajin aikin ba gaskiya bane.

Ya kara da cewa, labaran da ake yadawa na cewa gwamnatin tarayya ta sakar musu kudi har naira biliyan 30 ba gaskiya bane.

Jigo a kungiyar ya yi bayanin cewa tattaunawar da ake yi tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya domin samun sasanci bai kammala ba kuma suna kan hakan ne.

Hakazalika, jigon kungiyar ya ce majalisar zartarwa ta kungiyar malaman jami'o'in ne kadai za ta iya sanar da janye yajin aikin.

Ya kara da cewa, hukuncin majalisar zartarwan kuwa dole a kai shi gaban kungiya domin tattaunawa, don haka ba zai yuwu ko shugaban kungiyar ya iya janye yajin aikin ba.

KU KARANTA: Matar aure ta gurfana gaban kotu bayan ta soka wa makwabciya wuka a kai

Da duminsa: ASUU ta bayyana matsayarta a kan yajin aiki
Da duminsa: ASUU ta bayyana matsayarta a kan yajin aiki. Hoto daga Dailypost.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: FG da gwamnonin arewa maso yamma sun hada kai wurin kawo karshen 'yan bindiga

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum a ranar Alhamis ya ziyarci karamar hukumar Jere inda ya raba kayan abinci ga iyalai 5,000 mabukata, ya duba yadda wasu ayyuka uku suke tafiya da kuma karfafa wa sojoji guiwa.

Zulum ya kai ziyara zuwa Gongulong Lawanti, Khaddamari da Zabarmari duk a cikin karamar hukumar Jere.

A Gongulong Lawanti, gwamnan ya raba kayan abinci ga iyalai 4,000 yayin da wasu iyalan 1,000 suka amfana da tallafin a Khaddamari. Zulum ya ziyarci Zabarmari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel