Hotunan yadda rundunar soji ta cafke masu safarar shinkafa daga shiyyar Kudu maso Kudu

Hotunan yadda rundunar soji ta cafke masu safarar shinkafa daga shiyyar Kudu maso Kudu

- Rundunar soji da ke atisayen SILENT HEAT III sun samu babbar nasara a dalike laifukan da suka shafi karya tattalin arzikin kasa

- Dakarun sojin sansancin IBAKA, sun gudanar da ran gadi a tekun Utan Iyata, inda suka cafke buhuna 1,637 mai nauyin kilo giram 50

- Haka zalika rundunar ta cafke mutane 2 da ta ke zargin su ne suka yi safarar cinkafar daga Kamaru zuwa Nigeria

A ci gaba da dakile laifukan da suka shafi karya tattalin arziki da sauran laifuka makamantan su a shiyyar Kudu maso Kudu, dakarun atisayen SILENT HEAT III ta samu babbar nasara.

A ranar Asabar, dakarun da ke sansanin soji na IBAKA a jiragen su na ruwa sun cafke wani babban jirgi dauke da buhunan shinkafa a hanyar Utan Iyata da aka yi safarar ta daga Kamaru.

Rundunar sojin a cikin wata sanarwa daga Manjo Janar John Enenche, kodinetan watsa labarai na atisayen rundunar, ta bayyana cewa ta cafke mutane 2 da ke da hannu a safarar shinkafar.

KARANTA WANNAN: Rundunar soji za ta fara atisayen murmushin kada a fadin Nigeria

Hotunan yadda rundunar soji ta cafke masu safarar shinkafa daga shiyyar Kudu maso Kudu
Hotunan yadda rundunar soji ta cafke masu safarar shinkafa daga shiyyar Kudu maso Kudu - Defence Headquarters Nigeria
Asali: Facebook

Sanarwar ta ce, an cafke mutanen ne dauke da buhunan shinkafa 1,637 mai nauyin kilo giram 50, kuma ana zargin sun yo safararta daga Kamaru zuwa cikin Nigeria.

Rundunar sojin ta ce tuni ta gano ko su waye mutanen, kuma za ta mika su ga hukumar hana fasa kwabri da ke a cikin atisayen SWIFT RESPONSE domin yin bincike a kansu da shinkafar.

Haka zalika, rundunar ta jinjinawa dakarun da suka fita wannan ran gadi da kuma kara masu kwarin guiwa akan dagewa kan yaki da karya tattalin arziki a kasar.

Ga hotunan nasarar da rundunar ta samu a kasa:

Hotunan yadda rundunar soji ta cafke masu safarar shinkafa daga shiyyar Kudu maso Kudu
Hotunan yadda rundunar soji ta cafke masu safarar shinkafa daga shiyyar Kudu maso Kudu - Defence Headquarters Nigeria
Asali: Facebook

Hotunan yadda rundunar soji ta cafke masu safarar shinkafa daga shiyyar Kudu maso Kudu
Hotunan yadda rundunar soji ta cafke masu safarar shinkafa daga shiyyar Kudu maso Kudu - Defence Headquarters Nigeria
Asali: Facebook

Hotunan yadda rundunar soji ta cafke masu safarar shinkafa daga shiyyar Kudu maso Kudu
Hotunan yadda rundunar soji ta cafke masu safarar shinkafa daga shiyyar Kudu maso Kudu - Defence Headquarters Nigeria
Asali: Facebook

Hotunan yadda rundunar soji ta cafke masu safarar shinkafa daga shiyyar Kudu maso Kudu
Hotunan yadda rundunar soji ta cafke masu safarar shinkafa daga shiyyar Kudu maso Kudu - Defence Headquarters Nigeria
Asali: Facebook

A wani labarin, Rundunar soji ta ce za ta fara sabon atisayen murmushin kada a fadin Nigeria.

Atisayen kamar yadda ya ke a al'adance, ana gudanar da shi ne a karshen watanni uku na kowacce shekara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel