Gwamna Lalong ya jinjinawa UN wurin tabbatar da zaman lafiya a arewa maso gabas

Gwamna Lalong ya jinjinawa UN wurin tabbatar da zaman lafiya a arewa maso gabas

- Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, ya nuna farincikinsa akan yadda majalisar dinkin duniya ta taimaki jiharsa

- Gwamnan ya ce majalisar ta taka babbar rawa wurin kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a Plateau

- Yace yanzu haka gwamnatin jihar na kokarin ganin ta shawo kan tabarbarewar arziki sakamakon COVID-19, kuma yasan majalisar za ta taimaka

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya yabi majalisar dinkin duniya akan kokarinta wurin kawo zaman lafiya a Najeriya, musamman a arewa maso gabas.

Yace hakika shigar majalisar cikin al’amarin ya haifar da 'da mai ido.

Yace jihar Filato tana fuskantar matsalar rashin tsaro amma tun bayan majalisar ta sa baki al’amura suka fara daidaita.

Gwamnan yace, “A tarihi, jiharmu ce jihar farko da kungiyar ta fara samar wa zaman lafiya.”

A cewar Lalong “Ta sanadin kungiyar, mazauna anguwanni dakansu suke kwantar da tarzoma Idan ta tashi."

Ya Kara da cewa, “Yanzu haka jiharmu na kokarin ganin ta shawo kan tabarbarewar harkokin arziki sakamakon annobar COVID-19 da ta sa komai ya tsaya cak! . Na tabbatar majalisar dinkin duniya zata taimaka mana."

KU KARANTA: Turmi da tabarya na kama ta da babban abokina - Magidanci ya sanar da kotu

Gwamna Lalong ya jinjinawa UN wurin tabbatar da zaman lafiya a arewa maso gabas
Gwamna Lalong ya jinjinawa UN wurin tabbatar da zaman lafiya a arewa maso gabas. Hoto daga @Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSWAT: FG tana tunanin matasa, damuwarku tana damunmu - Osinbajo

A wani labari na daban, wasu daga cikin gwamnonin arewa, suna jin dadin ayyukan da SARS keyi kamar yadda shugaban kungiyar gwamnonin arewa ya bayyana.

Gwamnan jihar Filato, Gwamna Simon Lalong ya bayyana ra'ayin gwamnonin arewacin Najeriya.

Shugaban kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya sanar da manema labaran gidan gwamnatin hakan.

Lalong ya sanar da hakan bayan yayi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bayani akan halin rashin tsaro da jiharsa ke fuskanta, har ya sanar da Shugaba Buhari akan NAFEST dake matsowa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel