FG da gwamnonin arewa maso yamma sun hada kai wurin kawo karshen 'yan bindiga

FG da gwamnonin arewa maso yamma sun hada kai wurin kawo karshen 'yan bindiga

- Wakilan gwamnatin tarayya sun yi wani taro da masu ruwa da tsaki a jihar Katsina, ranar Alhamis

- Sun yi taron domin tattauna yadda za’a nemo bakin zaren yaki da ta’addanci a arewa

- Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, yace gwamnatin Buhari ta kusa kawo karshen ta’addanci a Najeriya

Waikilan gwamnatin tarayya sun yi wani taro a ranar Alhamis a Katsina a inda suka yi magana akan yadda za’a bullowa matsalar rashin tsaro da rikicin dake jihar da arewacin Najeriya.

Gwamnati tace sun yi taron ne don kokarin kawo karshen ta’addanci, garkuwa da mutane, satar shanu da sauran matsalolin dake addabar Najeriya musamman a arewa maso gabas.

Kakakin ma’aikatar harkokin cikin gida, Mohammed Manga, ya sanar da Hajajju a wata takarda a Abuja.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, a lokacin da yake magana a taron, yace matsalar ta’addanci a arewa maso yamma ta karu a shekaru 10 da suka gabata kuma matsalar ce tafi ci wa gwamnati tuwo a kwarya.

Aregbesola yace yaje taron da aka yi a Katsina ne saboda neman hadin kan gwamnati da mutanen Katsina don ganin an kawo karshen ta’addanci kuma rayuwar mutane ta koma kamar yadda take a da.

A cewar ministan, “Inada tabbacin gwamnatin Buhari zata kawo karshen ta’addanci a Najeriya”

KU KARANTA: EndSWAT: FG tana tunanin matasa, damuwarku tana damunmu - Osinbajo

FG da gwamnonin arewa maso yamma sun hada kai wurin kawo karshen 'yan bindiga
FG da gwamnonin arewa maso yamma sun hada kai wurin kawo karshen 'yan bindiga. Hoto daga @Dailynigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Turmi da tabarya na kama ta da babban abokina - Magidanci ya sanar da kotu

A wani labari na daban, wasu daga cikin gwamnonin arewa, suna jin dadin ayyukan da SARS keyi kamar yadda shugaban kungiyar gwamnonin arewa ya bayyana.

Gwamnan jihar Filato, Gwamna Simon Lalong ya bayyana ra'ayin gwamnonin arewacin Najeriya.

Shugaban kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya sanar da manema labaran gidan gwamnatin hakan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel