Gwamantin Buhari ta bayyana sabbin hanyoyin da za ta samu kudaden shiga
- Ministar kudi, Dr. Zainab Ahmed, ta bayyana cewa gwamnatin Buhari na ci gaba da gano hanyoyin samawa kasar kudaden shiga
- Ahmed ta bayyana cewa, babbar matsalar da ke addabar gwamnati a yau shine rashin kudaden shiga don gudanar da manyan ayyuka
- Ministar kudi ta kara da cewa rufe iyakokin Nigeria ya kawo babban ci gaba ga tattalin arziki, musamman ta fuskar noman shinkafa yar gida
Ministar kudi, kasafi da tsare tsaren kasa, Dr. Zainab Ahmed, a ranar Laraba, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da gano hanyoyin samawa kasar kudaden shiga.
Da ta ke jawabi a taron tattalin arzikin Nigeria karo na 26, Ahmed ta bayyana cewa, babbar matsalar da ke addabar gwamnati a yau shine rashin kudaden shiga don gudanar da manyan ayyuka.
Sai dai, ta yi nuni da cewa gwamnati ta damu matuka kan yadda za ta samar da yanayi mai kyau musamman na kusuwanci ta yadda farashin cinikayya zai ragu, da kuma samar da ayyukan yi.
KARANTA WANNAN: An tashi baram baram a ganawar ASUU da FG kan janye yajin aiki

Asali: UGC
"Samar da kudaden shiga shine babban aikin da ya rataya a wuyan gwamnati domin tabbatar da aiwatar da tsare tsaren da za su samar da ci gaban kasar ba ki daya.
"Kamar yadda kuka sani, babbar matsalar da gwamnati ta ke fuskanta ita ce matsalar rashin kudaden shiga da za su isa a aiwatar da manyan ayyukan raya kasa da sauran shirye shirye.
"Amma zuwa yanzu, mun yi binciken hanyoyin da za mu samu kudaden shiga. Mun bunkasa tsarin karbar haraji daga hukumomin tattara harajin," a cewar ta.
KARANTA WANNAN: Kyawawan hotunan matasa 12 da suka hadu a wajen bautar kasa kuma suka yi aure
Ministar kudi ta kara da cewa ci gaba da rufe iyakokin kasar Nigeria ya kawo babban ci gaba ga tattalin arzikin Nigeria, musamman ta fuskar samar da wadatacciyar shinkafa yar gida.
Ta ce: "A bangaren gwamnatin tarayya, rufe iyakokin kasa shine babban matakin da ta taba dauka, don magance matsalar tsaro, safara ba bisa ka'ida ba da kuma garkuwa da mutane."
Ta kara da cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da samar da dokoki da tsare tsare kan yadda kasar za ta shiga sahun na 100 a kasashe masu saukin kasuwanci a duniya.
A wani labarin, an tashi baram baram a zaman sulhu tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami'o'i (ASUU).
Kungiyar malaman jami'o'i da gwamnatin tarayya sun shiga ganawa a ranar Alhamis, da zummar kawo karshen yajin aikin da kungiyar ta shiga.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng