Ganduje ya umarci dan majalisa da ya dakata da wani gagarumin aikin mazabarsa

Ganduje ya umarci dan majalisa da ya dakata da wani gagarumin aikin mazabarsa

- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya dakatar da wani aikin titin tarayya a jihar

- Titin Rimingado zuwa Gulu ya kasance babban kalubale ga jama'ar yankin manoma dankalin

- Jobe ya tabbbatar da cewa gwamnan ya kira shi inda ya bukaci su dakata da aiki ko an kama su

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya umarci dan majalisa mai wakiltar Dawakin Tofa da Rimin Gado a tarayya, Tijjani Jobe, da ya dakata da wani aikin titi da ya fara a mazabarsa.

Babban tiitin Rimingado zuwa Gulu ya kasance cikin wani mawuyacin hali sama da shekaru 30, duk da kuwa amfaninsa ga jama'ar Gulu masu noman dankali da sauran mazauna yankin.

Tun farko dai dan majalisar ne ya mika bukatar aiki ga ma'aikatar noma ta tarayya a matsayin tallafin korona ga yankunan karkara.

Amman kuma jaridar Daily Nigerian ta gano cewa gwamnan na son samun jinjinar aiki duk da 'yan kwangilar tarayya sun fara aikin.

Daily Nigerian ta gano cewa gwamnan ya kira Jobe a ranar Talata a waya kuma ya umarcesa da ya kwashe 'yan kwangila su bar wurin ko kuma ya bada umarnin a kama su.

A hirar da Daily Nigerian ta yi da Jobe, ya tabbatar da cewa gwamna ne ya bada umarnin tsayar da aikin kuma ya hana su cigaba.

Kamar yadda yace, gwamnatin jihar ta bai wa wasu 'yan kwangila umarnin cigaba da aikin ba tare da sun duba wurin yadda ya dace ba.

A lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun Ganduje, Aminu Yassar, ya ce bai san aikin da ake magana ba.

Yassar ya ce yana da tabbacin cewa gwamnan ba zai hana aiwatar da wani aiki da ya san zai amfani jama'a ba.

"Koda da kamshin gaskiya a lamarin, tabbas an dakatar da aikin ne saboda wata bukata ta jama'a. Zai yuwu ya kasance barazana ga rayuka ko kuma akwai wata sarkakiya wurin biyan jama'ar da ke yankin," yace.

KU KARANTA: 'Yan sa kai sun kashe mutum 11 da ake zargi da zama 'yan bindiga a Katsina

Ganduje ya umarci dan majalisa da ya dakata da wani gagarumin aikin mazabarsa
Ganduje ya umarci dan majalisa da ya dakata da wani gagarumin aikin mazabarsa. Hoto daga @Dailynigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da albashinsa, dan majalisar tarayya ya gina katafariyar makaranta, ya zuba kayan bukata

A wani labari na daban, wasu daga cikin gwamnonin arewa, suna jin dadin ayyukan da SARS keyi kamar yadda shugaban kungiyar gwamnonin arewa ya bayyana.

Gwamnan jihar Filato, Gwamna Simon Lalong ya bayyana ra'ayin gwamnonin arewacin Najeriya. Shugaban kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya sanar da manema labaran gidan gwamnatin hakan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel