Turmi da tabarya na kama ta da babban abokina - Magidanci ya sanar da kotu

Turmi da tabarya na kama ta da babban abokina - Magidanci ya sanar da kotu

- Amzat Ibrahim mawaki ne kuma mazaunin garin Ibadan da ke jihar Oyo

- Ya tabbatar wa da kotu cewa turmi da tabarya ya kama matarsa da amininsa

- Ya sanar da yadda matarsa ta kwashe yaransa na tsawon wata uku amma sai a gidan abokinsa ya ganta

Wani mawaki mai suna Amzat Ibrahim, a ranar Alhamis ya sanar da wata kotun gargajiya da ke zama a Ile-Tuntun a Ibadan cewa matarsa fasika ce.

Ya sanar da yadda matarsa mai suna Zainab take lalata da babban amininsa.

Amzat ya bayyana wannan zargin ne bayan Zainab ta sanar da kotun cewa yana farautar rayuwarta domin haka take so a raba aurensu.

"Mai shari'a, a gaskiya ni da Zainab muna fada ne saboda halin bin mazanta. Zainab da babban abokina suna fasikanci.

“Ta yi batan dabo na tswon watanni uku inda ta bar gidana. Ta kwashe yarana amma daga bisani sai na gano tana gidan abokina ne kuma amini.

"Dumu-dumu na kama su suna faskancin," Amzat yace.

Kamar yadda mai karar wacce ta mallaki mashaya ta fara sanar da kotun, ta ce mijinta yana barazanar raba ta da rayuwarta.

Ta zargesa da tozartata tare da zaginta a cikin jama'a da kuma cikin gari.

"A koda yaushe yana bibiyar duk inda naje," matar ta sanar.

Alkalin kotun, Chief Henry Agbaje, ya shawarci ma'auratan da su tabbatar da ikirarinsu nan gaba a gaban kotun. Ya ce kowannensu ya bayyana da 'yan uwansa biyu a zama na gaba.

Ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 2 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA: Da albashinsa, dan majalisar tarayya ya gina katafariyar makaranta, ya zuba kayan bukata

Turmi da tabarya na kama ta da babban abokina - Magidanci ya sanar da kotu
Turmi da tabarya na kama ta da babban abokina - Magidanci ya sanar da kotu. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnonin jihohi 19 na arewa sun yi watsi da rushe rundunar SARS

A wani labari na daban, Belinda Effa, jarumar Nollywood ta wallafa hoton wata mata wanda ya ba kowa dariya.

A Bidiyon, wata mata ce a cikin jirgin sama, wadda ta bukaci a dakata da tashin jirgin don ta fita, saboda bata so a ajiye mata jakarta mai tsada a kasa ko kuma a ajiye jakar a ma'ajiyar cikin jirgin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel