Gwamnonin jihohi 19 na arewa sun yi watsi da rushe rundunar SARS

Gwamnonin jihohi 19 na arewa sun yi watsi da rushe rundunar SARS

- Wasu daga cikin gwamnonin arewa suna jin dadin ayyukan da SARS ke yi, saboda yanayin tsaron jihohinsu

- Shugaban kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan Plateau, Simon Lalong ya sanar da manema labaran gidan gwamnati hakan a ranar Alhamis

- A cewar Lalong, SARS na yin ayyukansu yadda ya kamata, shi bai ga dalilin rusa su ba, kamata yayi a gyara ayyukan nasu

Wasu daga cikin gwamnonin arewa, suna jin dadin ayyukan da SARS keyi kamar yadda shugaban kungiyar gwamnonin arewa ya bayyana.

Gwamnan jihar Filato, Gwamna Simon Lalong ya bayyana ra'ayin gwamnonin arewacin Najeriya.

Shugaban kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya sanar da manema labaran gidan gwamnatin hakan.

Lalong ya sanar da hakan bayan yayi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bayani akan halin rashin tsaro da jiharsa ke fuskanta, har ya sanar da Shugaba Buhari akan NAFEST dake matsowa.

Gwamnan yace bai dace a rushe SARS ba, kamata yayi a gyara aikin nasu. tare da inganta shi baki daya.

A cewarsa, SARS na iyakar kokarinsu wurin yin ayyukansu yadda ya dace.

KU KARANTA: Borno: 'Yan gudun hijira sun koka da rashin samun abinci

Gwamnonin jihohi 19 na arewa sun yi watsi da rushe rundunar SARS
Gwamnonin jihohi 19 na arewa sun yi watsi da rushe rundunar SARS. Hoto daga newswirengr.com
Asali: UGC

KU KARANTA: GP ya kaddamar da sabuwar makarantar 'ya'yan 'yan sanda a Daura

A wani labari na daban, wani al'amari mai firgitarwa ya faru a ranar Talata, 13 ga watan Oktoba 2020, inda wasu mutane masu makamai suka yi wa 'yan Kano fashi.

Jaridar Sahelian Times ta ruwaito yadda katti 4, majiya karfi suka yi wa mutane fashi a SHY Plaza a Gadon Kaya wuraren karfe 8:30 na dare.

'Yan fashin sun iso Plazar ne a cikin wata mota kirar Golf, kuma sun tsaya a Tukuntawa, wani yankin jihar Kano kusan a jejjere, inda suka rikitar kuma suka yi wa mazauna yankin fashi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel