Taka leda: Neymar ya aika wa Cristiano Ronaldo wasika bayan kamuwa da cutar COVID-19

Taka leda: Neymar ya aika wa Cristiano Ronaldo wasika bayan kamuwa da cutar COVID-19

- Tauraron dan wasan Brazil, Neymar ya aika da sakon jaje ga Cristiano Ronaldo, bayan kamuwa da cutar COVID-19

- Hukumar PFF a ranar Laraba ta sanar da cewa Ronaldo ya kamu da cutar kuma ya na killace a gidansa, sannan zai rasa wasa tsakaninsu da Sweden

- A wani ci gaban, kocin Brazil, Tite ya jinjinawa hazakar da Neymar ya ke nunawa, inda ya yi masa kirari da "Kwari da baka" na 'yan kwallo

Tauraron dan wasan Brazil, Neymar ya aika da sakon jaje ga Cristiano Ronaldo, bayan da labari ya fita na cewar Ronaldo ya kamu da cutar COVID-19 a ranar Laraba.

Hukumar kula da kwallon kafar Portuguese (PFF) a jiya ta sanar da cewa Ronaldo na killace a gidansa, kuma zai rasa wasan ranar Laraba tsakaninsu da Sweden a gasar NL.

Sai dai, har yanzu Ronaldo bai nuna wata alama ta yaduwar kwayar cutar a jikinsa ba, kamar yadda hukumar PFF ta tabbatar.

KARANTA WANNAN: Kyawawan hotunan matasa 12 da suka hadu a wajen bautar kasa kuma suka yi aure

Taka leda: Neymar ya aika wa Cristiano Ronaldo wasika bayan kamuwa da cutar COVID-19
Taka leda: Neymar ya aika wa Cristiano Ronaldo wasika bayan kamuwa da cutar COVID-19 - Goal.com
Asali: UGC

Da jin wannan labarin, Nyemar ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Dukkanin girmamawa ta ga wannan gwarzon"

A wani ci gaban, shugaban masu horas da 'yan wasa na Brazil, Tite ya jinjinawa hazakar da Neymar ya ke nunawa, yana mai cewa, dan wasan zai ci gaba da baje fasaharsa a nan gaba.

"A kowanne irin lokaci na tarin wannan kungiyar ta kasa, kowanne karni, na da na shi muhimmiancin," cewar Tite.

KARANTA WANNAN: Buhari zai ruguza EFCC da ICPC, ya bayyana dalili

"Kungiyar tana da Ronaldo, shi din na daban ne. Mun taba samun Rivaldo, Romario, Bebeto. Kowannensu ya ci lokacinsa. Zai zama rashin adalci kwatanta su a kwarewa.

"Abun da kawai zan iya cewa shine, shima Neymar na da ta shi baiwar ta musamman. Shi tamkar kwari da baka ne.

"Shi dan wasa ne mai ba da tallafi wajen cin kwallo kuma ya kware a taba zare, kuma kullum kara girmama ya ke yi, kamalarsa da kwarewarsa na kara bunkasa."

A wani labarin, Aisha Yesufu, ta bukaci matasan Nigeria da kada su karaya a kokarinsu na kawo sauyi a rundunar 'yan sandan kasar.

Yesufu ta yi wannan kiran ne a yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana a zanga zangar #EndSARS da matasan su ke yi, don karfafa mata guiwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel