Bidiyon budurwa ta tsayar da jirgin sama sannan ta sauka saboda ba za ta iya ajiye jakarta mai tsada ba a kasa

Bidiyon budurwa ta tsayar da jirgin sama sannan ta sauka saboda ba za ta iya ajiye jakarta mai tsada ba a kasa

- Jarumar Nollywood, Belinda Effa ta wallafa hotunan wata jaka da mai ita ta dakatar da jirginsu daga tashi saboda tsabar tsadar jakar

- Jarumar tayi bayani akan yadda mai jakar tace ta gwammaci ta sauka daga jirgin saman akan a ajiye mata jakarta mai tsada a kasa ko a ma'ajiyar dake cikin jirgin

- Dole aka dakatar da tashin jirgin, jami'an tsaron dake cikin jirgin suka fitar da ita waje, inda masu wucewa suka yi ta daukar hotuna a wayoyinsu

Belinda Effa, jarumar Nollywood ta wallafa hoton wata mata wanda ya ba kowa dariya.

A Bidiyon, wata mata ce a cikin jirgin sama, wadda ta bukaci a dakata da tashin jirgin don ta fita, saboda bata so a ajiye mata jakarta mai tsada a kasa ko kuma a ajiye jakar a ma'ajiyar cikin jirgin.

Wannan al'amarin ya dauki hankulan mutane, inda aka ga mutane masu wucewa duk sun fito da wayoyinsu don daukar wannan al'amarin mai ban dariya.

Jarumar wadda take a cikin jirgin da al'amarin ya faru ta wallafa a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram, inda tace, "Kun ga hoton jakar da ta dakatar da jirginmu daga tashi. Mai jakar ta dakatar da jirginmu saboda bata so a ajiye mata jakarta mai bala'in tsada a kasa ko a ma'ajiyar dake cikin jirgin.

"Sai da aka dakata, jami'an tsaron dake cikin jirgin suka raka ta waje, na kusa fasa wayata wurin daukan ta, saboda Inaso in nuna wa duniya jaka mai tsadar da ta dakatar da tafiyar mu."

KU KARANTA: FEC ta amince da fitar da N8 biliyan don titin Kano zuwa Maiduguri

Bidiyon budurwa ta tsayar da jirgin sama sannan ta sauka saboda ba za ta iya ajiye jakarta mai tsada ba a kasa
Bidiyon budurwa ta tsayar da jirgin sama sannan ta sauka saboda ba za ta iya ajiye jakarta mai tsada ba a kasa. Hoto daga @belindaeffah / IG.
Asali: Instagram

KU KARANTA: 'Yan sa kai sun kashe mutum 11 da ake zargi da zama 'yan bindiga a Katsina

A wani labari na daban, Gwamnatin tarayya na kokarin rage rashin aikin yi a Najeriya, inda ta bayar da adireshin yanar gizo da matasa zasu samu damar samun jari, don tallafawa masu kananan sana'o'i.

Hadimar shugaba Buhari, Laureta Onochie ta sanar da hakan a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoba ta kafar sada zumuntar zamani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel