'Yan sa kai sun kashe mutum 11 da ake zargi da zama 'yan bindiga a Katsina

'Yan sa kai sun kashe mutum 11 da ake zargi da zama 'yan bindiga a Katsina

- Ta'addanci ya nunku a karamar hukumar Kurfi dake jihar Katsina saboda kashe Fulani 11 da 'yan Sa kai suka yi a Dutsin Karare

- Jaridar ThisDay, ta wallafa yadda 'yan Sakai suka je har kasuwar Wurmo, inda suka kwashe Fulanin da ake zargin 'yan Bindiga ne, suka yi musu yankan rago

- Tuni Hukumar 'yan Sandan jihar Katsina ta bazama da neman 'yan Sa kan da suka yi wannan mummunan aikin don su fuskanci fushin hukuma

Ta'addanci ya barke a karamar hukumar Kurfi da ke jihar Katsina, bayan 'yan Sa kai sun kashe wasu Fulani 11 da ake zargin 'yan bindiga ne.

An zargi matasan fulanin da zama 'yan bindigan da ke addabar kananan hukumomin Kurfi, Dutsin-Ma da kuma Batsari dake jihar.

Gwamnan jihar, Aminu Bello Masari ya hana 'yan Sakai daukar mataki akan 'yan bindiga.

Jaridar ThisDay ta tattaro bayanai akan yadda 'yan Sa kai daga kananan hukumomin Kurfi da Batsari suka biyo Fulanin zuwa kasuwar Wurma a ranar Litinin, inda suka sunkucesu zuwa Dutsin Karare suka yi musu yankar rago.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah, yace ayyukan 'yan Sakai ne ke karo matsalolin rashin tsaro a jihar.

Tuni 'yan sanda sun bazama wurin bincike akan wadanda suka yi wannan kisar don su hukunta su, a cewar sa.

KU KARANTA: FG ta fitar da adireshin yanar gizo na samun tallafin matasa

'Yan sa kai sun kashe mutum 11 da ake zargi da zama 'yan bindiga a Katsina
'Yan sa kai sun kashe mutum 11 da ake zargi da zama 'yan bindiga a Katsina. Hoto daga @ThisDay
Asali: Twitter

KU KARANTA: FEC ta amince da fitar da N8 biliyan don titin Kano zuwa Maiduguri

A wani labari na daban, a makon da ya gabata, gwamnatin jihar Borno ta fara kokarin mayar da 'yan gudun hijira zuwa garuruwan su. Ma'aikatar gyara da mayar da 'yan gudun hijira gidajensu ce take jagorantar shirin.

AFP ta ruwaito yadda mayakan Boko Haram suka shiga gonaki kuma suka farma masu noman rani a kauyen Ngwon, wanda yake da tazarar kilomita 14 ta Arewa zuwa birnin Maiduguri.

'Yan Boko Haram din sun yanka wuyan manoman kuma sun yi musu alama ta masu jihadin Musulunci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel