IGP ya kaddamar da sabuwar makarantar 'ya'yan 'yan sanda a Daura

IGP ya kaddamar da sabuwar makarantar 'ya'yan 'yan sanda a Daura

- Sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Abubakar Adamu, ya kaddamar da makarantar yaran 'yan sanda a karamar hukumar Daura

- Makarantar tana da azuzuwa 32 don samar da ingantaccen ilimi cikin rahusa ga yaran 'yan sanda da fararen hula dake Daura da kewaye

- Dama makarantar nada sashi na wucin-gadi, amma sakamakon yawan dalibai, Gwamna Masari ya basu fili don yin ginin sashin dindindin

Sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Abubakar Adamu, ya kaddamar da makarantar yaran 'yansanda mai azuzuwa 32 a Daura, jihar Katsina.

IGP din ya samu wakilcin DIG dake kula da harkokin kudi da mulki, Abdul Dahiru Danwawu, yace an yi makarantar don mutanen dake unguwar ne ba saboda yaran 'yan sanda kadai ba.

DCP Rabi Umar, a jawabinta na maraba, tace an bude makarantar a watan Janairun 2017 a wani wuri na wucin-gadi, don samar da ilimi mai sauki da inganci ga yaran 'yan sandan dake Daura da kewaye.

Tace sakamakon yawan dalibai da makarantar tayi ta samu, sai suka ga ya dace ace anyi gini na dindindin, inda suka bukaci gwamna Aminu Bello Masari da ya basu fili, sai ya basu 1.008 acres na fili.

A jawabin Sarkin Daura, Alh. Faruk Umar Faruk, yayi godiya ga IGP da rundunar 'yan sandan Najeriya saboda karamcinsu, a inda yayi kira ga sauran ma'aikatun gwamnati tarayya da su yi koyi da su.

KU KARANTA: FEC ta amince da fitar da N8 biliyan don titin Kano zuwa Maiduguri

IGP ya kaddamar da sabuwar makarantar 'ya'yan 'yan sanda a Daura
IGP ya kaddamar da sabuwar makarantar 'ya'yan 'yan sanda a Daura. Hoto daga Katsinapost.com.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Ruwa ya yi awon gaba da 'yan mata uku a jihar Jigawa

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin tattaunawa da jama'a akan kawo karshen rikicin 'yan bindiga da sauran tashin hankali da 'yan Najeriya ke fuskanta.

Kakakin ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya ce gwamnati na bukatar jin ta bakin 'yan kasa, don samun yadda za ta kamo bakin zare akan harkokin tsaro, yayin da yake bude wani taro a Maiduguri.

A cewarsa, "Kamar yadda wasu kasashe suka fuskanci irin wannan matsalar, kuma suka kawo karshenta, wajibi ne mu nemi shawarar al'ummar Najeriya don magance wannan matsalar da ta addabemu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel