FEC ta amince da fitar da N8 biliyan don titin Kano zuwa Maiduguri

FEC ta amince da fitar da N8 biliyan don titin Kano zuwa Maiduguri

- Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da karin Naira bilyan 8 akan kudin gyaran titin da ya wuce ta wudil dake jihar Kano zuwa Maiduguri mai tsawon Kilomita 560

- Dama ministan aiki da gidaje, Babatunde Fashola ya bukaci naira biliyan 63 ne, daga baya ya bukaci karin biliyan 8 akan hakan don aikin ya tabbata

- Ba titin Kano zuwa Maiduguri kadai majalisar ta amince da bayar da kwangilar gyaran shi ba, har da na Apapa-Oworonsoki-Ojota Phase section II, wanda ya bukaci naira 22,247,332,000

Majalisar zartarwa ta tarayya wadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jagoranta ta amince da karin Naira Biliyan 8 don tagwaita titin Kano zuwa Maiduguri wanda ya ratsa ta Wudil.

Ministan yada labarai, Lai Mohammed ya sanar da hakan bayan taron sati da aka yi ranar Laraba, inda yace an kiyasta kashe naira biliyan 63 don aikin titin Kano zuwa Maiduguri wanda ya mike dodar na tsawon Kilomita 560.

Mohammed yace ministan ayyuka da muhalli, Babatunde Fashola ya nemi karin naira biliyan 8 don aikin ya tabbata, wadda majalisar ta amince.

Ministan yace, majalisar ta amince da bayar da Naira 22,247,332,000 don gyara titin Apapa-Oworonsoki-Ojota Phase II, wanda tsayinshi ya kai kilomita 8.1.

A cewar Mohammed: "Inaso in sanar daku cewa Fashola ya gabatar wa da majalisa kwangilar gyaran titin Apapa-Oworonsoki-Ojota Phase Section II, wanda yake bukatar karin fadin titin, na tsawon kilomita 8.1, kuma majalisar ta amince da hakan."

KU KARANTA: Tsaro: FG ta kaddamar sabon shirin tattaunawa da jama'a

FEC ta amince da fitar da N8 biliyan don titin Kano zuwa Maiduguri
FEC ta amince da fitar da N8 biliyan don titin Kano zuwa Maiduguri. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Borno: 'Yan gudun hijira sun koka da rashin samun abinci

A wani labari na daban, wasu 'yan gudun hijira dake jihar Borno, sun yi korafi akan rashin samun abinci da kuma zargin sojojin dake tsaresu da cutar da su.

'Yan gudun hijirar guda 37 da basu dade da kubutowa daga hannun 'yan bindiga ba, yanzu haka suna zaune a sansanin gudun hijira dake Dalori a babban birnin jihar, sun yi koke akan tsaka mai wuyar da suka tsinci kansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel