Zaben kananan hukumomi: Sarkin Kano ya roki lumana da kwanciyar hankali yayin zabe

Zaben kananan hukumomi: Sarkin Kano ya roki lumana da kwanciyar hankali yayin zabe

- Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero yayi kira ga 'yan Kano da su guji tada tarzoma a ranar zaben kananan hukumomi dake gabatowa

- Sarkin yayi wannan kiran ne a ranar Laraba, a lokacin da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Farfesa Garba ya kai masa ziyara Fada

- Inda Farfesa Garba yake sanar dashi cewa lallai an tsayar da ranar zaben kananan hukumomi ta zama ranar 16 ga watan Janairun 2021

Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, a ranar Laraba, ya roki al'ummarsa da su yi zaben gaskiya da gaskiya a zaben dake gabatowa na kananan hukumomi wanda za'ayi ranar 16 ga watan Janairu 2021 a Kano.

Yayi wannan kiran ne lokacin da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Farfesa Garba Ibrahim Sheka da mutanensa suka je fadar sarkin don sanar dashi ranar zabe da aka tsayar.

Sarki Bayero ya roki duk wani mai fadi a ji akan harkar zabe da yayi kokarin tabbatar da an yi zabe cikin lumana.

Kamar yadda yace, "Jam'iyyu da masu sabanin ra'ayi su yi iya kokarinsu don tabbatar da basu yi wata magana ko kuma wani abu da zai kawo tarzoma ba."

Sarkin Kano ya kara da cewa, "Kowa ya san yadda jihar Kano ta zama madubin dubawar jihohi da dama, ina mai rokon duk wani dan Kano da ya guji abinda zai iya kawo fitina, tashin hankali ko kuma tarzoma a ranar zabe."

KU KARANTA: Borno: 'Yan gudun hijira sun koka da rashin samun abinci

Zaben kananan hukumomi: Sarkin Kano ya roki lumana da kwanciyar hankali yayin zabe
Zaben kananan hukumomi: Sarkin Kano ya roki lumana da kwanciyar hankali yayin zabe. Hoto daga Vanguard
Asali: UGC

KU KARANTA: Sabon harin Boko Haram: Rayukan manoma 14 sun salwanta

A wani labari na daban, wani al'amari mai firgitarwa ya faru a ranar Talata, 13 ga watan Oktoba 2020, inda wasu mutane masu makamai suka yi wa 'yan Kano fashi.

Jaridar Sahelian Times ta ruwaito yadda katti 4, majiya karfi suka yi wa mutane fashi a SHY Plaza a Gadon Kaya wuraren karfe 8:30 na dare.

'Yan fashin sun iso Plazar ne a cikin wata mota kirar Golf, kuma sun tsaya a Tukuntawa, wani yankin jihar Kano kusan a jejjere, inda suka rikitar kuma suka yi wa mazauna yankin fashi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel