Tsaro: FG ta kaddamar sabon shirin tattaunawa da jama'a

Tsaro: FG ta kaddamar sabon shirin tattaunawa da jama'a

- Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin tattaunawa da 'yan Najeriya don magance matsalar rashin tsaro

- Ministan harkokin cikin gida yace wajibi ne a hada karfi da karfe wurin neman yadda za'a bullo wa rashin tsaro a Najeriya

- Yace ana bukatar shawarwari daga bakin 'yan Najeriya da kuma hadin kai don ganin karshen wannan matsala da ta damu kowa

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin tattaunawa da jama'a akan kawo karshen rikicin 'yan bindiga da sauran tashin hankali da 'yan Najeriya ke fuskanta.

Kakakin ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya ce gwamnati na bukatar jin ta bakin 'yan kasa, don samun yadda za ta kamo bakin zare akan harkokin tsaro, yayin da yake bude wani taro a Maiduguri.

A cewarsa, "Kamar yadda wasu kasashe suka fuskanci irin wannan matsalar, kuma suka kawo karshenta, wajibi ne mu nemi shawarar al'ummar Najeriya don magance wannan matsalar da ta addabemu."

Ya kara da cewa, "Harkar tsaro al'amari ne mai rikitarwa, kuma hukumar 'yan sanda da Rundunar soji ne kadai suke iya bada ta."

A cewarsa, "Babu hukumar tsaro da zata samu nasara, matsawar 'yan kasa basu bayar da hadin kai ba."

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya bayar da tabbacin cewa mutanen jiharsa za su bai wa jami'an tsaro da gwamnatin tarayya cikakken hadin kai don kawo karshen rashin tsaro a jihar Borno.

KU KARANTA: EndSARS: Babu jinin dan Najeriya da ya cancanci zuba - Goodluck Jonathan

Tsaro: FG ta kaddamar sabon shirin tattaunawa da jama'a
Tsaro: FG ta kaddamar sabon shirin tattaunawa da jama'a. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Mun ware N200m domin rage wa iyalan wadanda aka kashe radadi - Sanwo-Olu

A wani labari na daban, wani al'amari mai firgitarwa ya faru a ranar Talata, 13 ga watan Oktoba 2020, inda wasu mutane masu makamai suka yi wa 'yan Kano fashi.

Jaridar Sahelian Times ta ruwaito yadda katti 4, majiya karfi suka yi wa mutane fashi a SHY Plaza a Gadon Kaya wuraren karfe 8:30 na dare.

'Yan fashin sun iso Plazar ne a cikin wata mota kirar Golf, kuma sun tsaya a Tukuntawa, wani yankin jihar Kano kusan a jejjere, inda suka rikitar kuma suka yi wa mazauna yankin fashi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel