Borno: 'Yan gudun hijira sun koka da rashin samun abinci

Borno: 'Yan gudun hijira sun koka da rashin samun abinci

- 'Yan gudun hijira dake zaune a sansanin gudun hijira na Dalori, dake babban birnin jihar Borno sun yi korafi akan yunwa da tsinkewar abinci

- 'Yan gudun hijiran sun ce yanzu haka suna tsaka mai wuya, dama tun da aka kaisu sansanin, watanni 3 kadai ne aka basu abinci, shima ba isasshe ba

- Bayan bakar wahalar da suka sha wurin 'yan Boko Haram, da kuma wurin sojojin da suka tabbatar basu da hadi da 'yan Boko Haram, ashe akwai sauran rina a kaba

Wasu 'yan gudun hijira dake jihar Borno, sun yi korafi akan rashin samun abinci da kuma zargin sojojin dake tsaresu da cutar da su.

'Yan gudun hijirar guda 37 da basu dade da kubutowa daga hannun 'yan bindiga ba, yanzu haka suna zaune a sansanin gudun hijira dake Dalori a babban birnin jihar, sun yi koke akan tsaka mai wuyar da suka tsinci kansu.

Sojoji sun sakosu ne a watan Nuwamban 2019, bayan tabbatar da cewa basu da wani hadi da Boko Haram.

Sun kuma yi kusan watanni 3 a babban asibitin Umaru Shehu don tabbatar da lafiyarsu. Amma tun da aka mayar da su sansanin gudun hijira suke azabtuwa.

Bayan sun yi korafi akan yunwa da kuma tsinkewar abinci, ma'aikatan IMF sun zo sansanin inda suka basu 6Kg na gero, rabin litar mangyada da kuma 4kg na wake, tsakanin watan Afirilu zuwa Yuni, tun daga nan suka daina basu komai.

Sun ce akwai fom da suke sa hannu a duk lokacin da aka basu kayan abincin, wanda suka sa hannu sau 3, daga nan basu kara ba.

A ranar Laraba, 7 ga watan Oktoba, ma'aikatan IMF sun zo sansanin don tattaunawa da 'yan gudun hijiran. Basu tarad da sauran ba sai mutane 16 daga cikin su, inda suka yiwa ma'aikatan bayanin cewa sauran sun tafi aikin neman na tuwo.

"Sun tambayemu tsawon lokacin da ba'a bamu abinci ba, inda muka sanar da su cewa watanni 3 kenan," inji Bura Bukar, mai shekaru 40.

"Sai suka ce mun lashe na watanni ukunnan, sai dai a dora daga inda aka tsaya, sannan abincin da za'a dinga bamu yanzu babu mangyada."

KU KARANTA: Bidiyon saurayi yana hana budurwa satar ruwan lemunsa a wurin cin abinci

Borno: 'Yan gudun hijira sun koka da rashin samu abinci
Borno: 'Yan gudun hijira sun koka da rashin samu abinci. Hoto daga @HumAngle
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: Bidiyon dan sanda yana zazzabga wa tsohuwa mari a wurin zanga-zanga

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasan Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan, yace bai dace a zubar da jinin wani dan Najeriya ba a saboda zanga-zangar lumana akan SARS.

Yace ya lura zanga-zangar da suke yi don ci gaban kasa suke yi, jaridar Vanguard ta wallafa hakan.

Tsohon shugaban kasan, yayi maganar ne a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda yake rokon tabbatar da adalci ga lamarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel