Da duminsa: An sace matar wani babban dan jarida a Calabar

Da duminsa: An sace matar wani babban dan jarida a Calabar

- Wasu da ake kyautata zaton cewa masu garkuwa da mutane ne sun sace matar wani babban dan jarida a jihar Cross River

- Tuni aka sanar da jami'an tsaro don daukar matakin gaggawa

- Rahotanni sun bayyana cewa wannan shine karo na biyu da ake sace matar a cikin 'yan shekarun nan

Wasu da ake kyautata zaton cewa masu garkuwa da mutane ne sun sace matar shugaban masu dauko rahotanni na kungiyar NUJ reshen jihar Cross River, Mazi Judex Okoro.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an sace matar ne da misalin karfe 8 na daren ranar Talata, a yankin Biq Qua, kusa da cocin Apostolic, karamar hukumar Calabar ta tsakiya.

Duk da cewa akwai rudani a cikin labarin sace ta a lokacin hada wannan rahoto, sai dai tuni aka sanar da jami'an tsaro, don daukar matakin gaggawa.

KARANTA WANNAN: Rundunar 'yan sandan Lagos ta kwace makamai daga hannun jami'an SARS

Da duminsa: An sace matar wani babban dan jarida a Calabar
Da duminsa: An sace matar wani babban dan jarida a Calabar - @vanguardngrnews
Asali: Twitter

Haka zalika, rahotanni sun bayyana cewa wannan ne karo na biyu da aka yi garkuwa da ita, a cikin 'yan shekarun nan.

Judex Okoro ya na aiki a matsayin wakilin jaridar The Sun a jihar Cross River, ya kuma tabbatar da sace matarsa a daren ranar Talata.

A wani labarin, Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda, Mohammed Adamu a ranar Talata ya umurci gaba daya jami'an da ke a sashen dakile fashi da makami SARS da su je shelkwatar rundunar da ke Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an idan sun je Abuja, za ayi masu gwajin kwakwalwa a shirye shiryen yi masu horo don rarrabasu zuwa wasu sashe sashe na rundunar.

KARANTA WANNAN: Na taba kwasar kashina a hannun 'yan sanda - Mataimakin gwmanan Oyo

A wani ci gaban, IGP ya samar da sashen jami'an da suka kware a sarrafa makamai da fada (SWAT) da zai cike gurbin korarren sashen jami'an SARS.

Mambobin wannan sabon sashen za su samu horo da kuma jarabawar kwakwalwa domin tabbatar da cewa za su iya gudanar da wannan muhimmin aiki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel