'Ku daina amfani da fitsari da kashin shanu wajen maganin ciwon idanu'

'Ku daina amfani da fitsari da kashin shanu wajen maganin ciwon idanu'

- Dr. Ibrahim Yuguda, ya gargadi 'yan Nigeria da su daina amfani da fitsari, gishiri, sukari ko ruwa da kashin shanu wajen magance ciwon idanu

- Likitan ya gargadi masu sayen maganin ciwon idanu ba tare da izinin likitoci ba, yana mai cewa yin hakan zai kara dagula lissafi ne ba wai kawo waraka ba

- A cewar Dr. Ibrahim, zuwa gwaji asibiti shine kadai mafita ta sanin lalurar idanun, da kuma yadda za a shawo kan matsalar da ta ke damun su

Wani kwararren likitan idanu a asibitin koyarwa na Aminu Kano, Dr. Ibrahim Yuguda, ya gargadi 'yan Nigeria da su daina amfani da fitsari da kashin shanu wajen magance ciwon idanu.

Da ya ke zantawa da manema labarai a bukin 'ranar gani' ta duniya a Kano, Yuguda ya ce babban kuskure ne amfani da sukari, gishiri, ruwa, fitsari ko kashin shanu don maganin ciwon idanu.

Ya bayar da shawarar cewa, zuwa gwaji asibiti shine kadai mafita ta sanin lalurar idanun, da kuma yadda za a shawo kan matsalar da ta ke damun su.

KARANTA WANNAN: Sabbin mutane 225 sun kamu da cutar COVID-19, mutane 1116 sun mutu

'Ku daina amfani da fitsari da kashin shanu wajen maganin ciwon idanu'
'Ku daina amfani da fitsari da kashin shanu wajen maganin ciwon idanu' - @daily_trust
Asali: Twitter

Ya kuma shawarci al'umma da su daina sayen maganin digawa a idanu ba tare da amincewar likita ba, yana mai cewa, yin hakan zai kara dagula lissafi ne ba wai gyara ba.

"Abun da ya kamata su yi shine zuwa gwaji asibiti domin sanin matsalar da kuma yadda za a shawo kanta tun da wuri.

"A duk fadin duniya, sama da mutane miliyan biyu ne ke fama da cutar makanta ko matsalar gani, daga mizanin babbar matsala zuwa karama.

"A kuma wani adadin, sama da mutane biliyan daya ne aka yi masu magani kuma suka warke, sakamakon yin gwaji da wuri," a cewar likitan.

Ya shawarci al'umma, musamman masu shekaru sama da 40, da su kokarta, su je a rika yi masu gwajin idanu sau daya a shekara, da shawarar cewa, maganin wuri ya fi aiki akan cuta.

A wani labarin, Adadin wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a Nigeria ya kai 60,655 a daren ranar Talata biyo bayan sabbin mutane 225 da suka kamu da cutar.

Hukumar da ke dakile yaduwar cututtuka ta Nigeria (NCDC) ta bayyana wadannan alkaluman a ranar 13 ga watan Oktoba, 2020 a shafinta na Twitter.

Jihar Lagos na da sabbin mutane 165 daga cikin 225, sai babban birnin tarayya Abuja da ke bin Lagos da mutane 17, yayin da Rivers ke da mutane 13.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel