Yanzu yanzu: Sabbin mutane 225 sun kamu da cutar COVID-19, mutane 1116 sun mutu

Yanzu yanzu: Sabbin mutane 225 sun kamu da cutar COVID-19, mutane 1116 sun mutu

Adadin wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a Nigeria ya kai 60,655 a daren ranar Talata biyo bayan sabbin mutane 225 da suka kamu da cutar.

Hukumar da ke dakile yaduwar cututtuka ta Nigeria (NCDC) ta bayyana wadannan alkaluman a ranar 13 ga watan Oktoba, 2020 a shafinta na Twitter.

Jihar Lagos na da sabbin mutane 165 daga cikin 225, sai babban birnin tarayya Abuja da ke bin Lagos da mutane 17, yayin da Rivers ke da mutane 13.

KARANTA WANNAN: Na taba kwasar kashina a hannun 'yan sanda - Mataimakin gwmanan Oyo

Yanzu yanzu: Sabbin mutane 225 sun kamu da cutar COVID-19, mutane 1116 sun mutu
Yanzu yanzu: Sabbin mutane 225 sun kamu da cutar COVID-19, mutane 1116 sun mutu - NCDCgov
Asali: Twitter

Sauran jihohin da aka samu sabbin masu dauke da cutar sun hada da: Ogun – 12, Niger – 8, Delta – 4, Ondo – 2, Anambra – 1, Edo – 1, Ekiti – 1, Kaduna – 1.

Adadin wadanda suka kamu da cutar a Nigeria ya zuwa yanzu ya kai 60,655, inda aka sallami mutane 52,006 bayan warkewa daga cutar.

Sai dai, annobar COVID-19 ta yi sanadiyar mutuwar mutane 1,116 a fadin kasar tun bayan barkewarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel