Ayyuka 774,000: Buhari ya sanar da ranar fara diban ma'aikata

Ayyuka 774,000: Buhari ya sanar da ranar fara diban ma'aikata

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bukatar karamin ministan kwadago da aikin yi

- Ministan ya bukaci a amince da samar da ayyuka ga mutane 1000 a kowacce karamar hukuma 774 da ke Najeriya

- Za'a fara shirya yadda al'amuran zasu wakana daga 1 ga watan Oktoba zuwa 1 ga watan Nuwamba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bukatar karamin ministan kwadago da aikin yi, Festus Keyamo, SAN, na samar da ayyuka na musamman daga ranar 1 ga watan Oktoba zuwa 1 ga watan Nuwamban shekarar 2020.

Tsarin zai kunshi samarwa mutane 1000 ayyukan watanni 3 daga kowacce karamar hukuma 774 dake kasar nan.

A takardar da ministan yasa hannu jiya Litinin, yace shugaban kasar ya amince da bukatar ta shi ne idan ruwa ya dauke, sai dai har yanzu ruwan bai dauke ba.

Yace "Za'a karasa shirya wuraren da za'a fara ayyukan a 1 ga watan Nuwamba," kamar yadda takardar ta zo.

KU KARANTA: Bidiyon saurayi yana hana budurwa satar ruwan lemunsa a wurin cin abinci

Ayyuka 774,000: Buhari ya sanar da ranar fara diban ma'aikata
Ayyuka 774,000: Buhari ya sanar da ranar fara diban ma'aikata. Hoto daga @Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Masu kamun kifi sun ceto matar da tayi shekara 2 da bacewa a cikin teku

A wani labari na daban, anyi wani kwarya-kwaryan rikici a majalisar jihar Edo, inda cikin 'yan majalisu 10, 9 suka hada karfi da karfe wurin tube kakakin majalisar, Hon Frank Okiye, sakamakon zargin shi da ake yi da barnar dukiyar al'umma.

Bayan sun tube shi, take-yanke suka zabi wani sabon kakakin majalisar mai suna Hon. Marcus Onobun, wanda ke wakiltar mazabar Esan ta kudu.

Bayan an rantsar dashi take ya rushe duk wata kwamiti sannan ya soke duk wasu nade-nade da tsohon kakakin yayi, inda ya samar da wata kwamitin mutane 3 da zasu kula da shige da ficen kudi a majalisar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel