EndSARS: Babu jinin dan Najeriya da ya cancanci zuba - Goodluck Jonathan

EndSARS: Babu jinin dan Najeriya da ya cancanci zuba - Goodluck Jonathan

- Tsohon shugaban kasan Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan, Yace bai dace a zubar da jinin wani ba akan zanga-zangar rushe SARS ba

- Yace 'yan Najeriya na yin wannan zanga-zangar lumanar ne don ci gaban Najeriya don haka bai dace ace an cutar da wani ba

- Ya kuma kara rokon 'yan Najeriya akan kowa ya kwantar da hankalinsa musamman a irin wannan lokacin na tsanani

Tsohon shugaban kasan Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan, yace bai dace a zubar da jinin wani dan Najeriya ba a saboda zanga-zangar lumana akan SARS.

Yace ya lura zanga-zangar da suke yi don ci gaban kasa suke yi, jaridar Vanguard ta wallafa hakan.

Tsohon shugaban kasan, yayi maganar ne a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda yake rokon tabbatar da adalci ga lamarin.

Kamar yadda Goodluck Jonathan ya wallafa, "Babu jinin dan Najeriyan da ya dace a zubar ta dalilin neman cigaban Kasarmu.

"Zamu iya yin tunani daban-daban akan al'amuran da suka shafi kasa, amma babu kuskure, kowanne dan Najeriya na son cigaban ta."

"Ina son kowa ya kwantar da hankalinsa musamman a wannan lokacin na tsanani," a cewar Goodluck.

KU KARANTA: Magidanci ya saka wa bishiyarsa raga domin hana makwabta amfana da ita

EndSARS: Babu jinin dan Najeriya da ya cancanci zuba - Goodluck Jonathan
EndSARS: Babu jinin dan Najeriya da ya cancanci zuba - Goodluck Jonathan. Hoto daga @Vanguard
Asali: UGC

KU KARANTA: Abubuwa 6 da ya kamata a sani game da sabuwar rundunar SWAT ta 'yan sanda

A wani labari na daban, fadar shugaban kasa tace an sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari akan zanga-zangar da matasa ke yi saboda kashe-kashen da jami'an SARS ke yi.

Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa akan harkokin watsa labarai ya sanar da hakan a ranar Juma'a, 9 ga watan Oktoba, matasa na tsaka da zanga-zanga akan kisan wulakanci da 'yan sanda ke yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel