Abubuwa 6 da ya kamata a sani game da sabuwar rundunar SWAT ta 'yan sanda

Abubuwa 6 da ya kamata a sani game da sabuwar rundunar SWAT ta 'yan sanda

- Sifeta janar na'yan sanda, Mohammed Adamu, ya kirkiri rundunar SWAT don maye gurbin 'yan sandan SARS

- Sifetan ya gindaya dokokin da za'a bi don horar da sababbin rundunar, ya kuma fadi wuraren da za'a horar dasu

- Sifetan ya bukaci duk 'yan sandan SARS da aka rushe su bayyana a hedkwatar 'yan sanda dake Abuja don a auna lafiyar kwakwalwar su

Sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu, ya kirkiri sabuwar runduna, Rundunar makamai da dabaru (SWAT) don maye gurbin 'yan sandan SARS.

A ranar Lahadin da ta gabata ne ya rushe SARS saboda kisan da suke yi ba tare da kotu ta bada umarni ba, da kuma cin zarafi da wulakanta mutane.

Ga abubuwa 6 da ya kamata ka sani game da wannan sabuwar rundunar da ya kirkira:

1. Za'a auna kwakwalwa da kuma lafiyar mambobin wannan kungiyar don tabbatar da lafiyarsu wurin aiwatar da aikinsu.

2. Mako mai zuwa za'a fara horar da wadannan sababbin mambobin a makarantun horar da 'yan sanda da ke Najeriya.

3. Makarantun da zasu horar da su sune;

A. Za'a horar da 'Yan kudu maso gabas da kuma 'yan kudu a kwalejin Counter-Tourism dake Nonwa a jihar Rivers

B. Za'a hara 'yan arewa a Police Mobile Force Training College a Ende, jihar Nasarawa

C. Wadanda ke kudu maso yamma za'a horar da su a Police Mobile Force Training College da ke Ila-Oragun a jihar Osun

4. Sifeta janar na 'yan sanda ya umarci duk wasu 'yan sandan SARS da aka rushe rundunarsu da su bayyana a hedkwatar 'yan sanda da ke Abuja, don dubasu da kuma tabbatar da lafiyar kwakwalwarsu.

5. Daga yanzu, PCSU ne zasu dinga tantancewa da kuma tabbatar da lafiyar kwakwalwar duk wasu jami'an rundunar da za'a dauka don yin ayyuka na musamman da sauransu.

6. Za'a dinga ajiye likitocin kwakwalwa, masu karantar hallayar dan Adam, fastoci da limamai, ma'aikatan lafiya, masu kare hakkin dan Adam da sauran ma'aikata don tantance wadanda za'a dauka a aikin 'yan sanda a PCSU din.

KU KARANTA: EndSARS: Bidiyon dan sanda yana zazzabga wa tsohuwa mari a wurin zanga-zanga

Abubuwa 6 da ya kamata a sani game da sabuwar rundunar SWAT ta 'yan sanda
Abubuwa 6 da ya kamata a sani game da sabuwar rundunar SWAT ta 'yan sanda. Hoto daga @Dailynigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Magidanci ya saka wa bishiyarsa raga domin hana makwabta amfana da ita

A wani labari na daban, an yi wani kwarya-kwaryan rikici a majalisar jihar Edo, inda cikin 'yan majalisu 10, 9 suka hada karfi da karfe wurin tube kakakin majalisar, Hon Frank Okiye, sakamakon zargin shi da ake yi da barnar dukiyar al'umma.

Bayan sun tube shi, take-yanke suka zabi wani sabon kakakin majalisar mai suna Hon. Marcus Onobun, wanda ke wakiltar mazabar Esan ta kudu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel