EndSARS: Bidiyon dan sanda yana zazzabga wa tsohuwa mari a wurin zanga-zanga

EndSARS: Bidiyon dan sanda yana zazzabga wa tsohuwa mari a wurin zanga-zanga

- Hakika abubuwa marasa dadin ji nata faruwa a Najeriya sakamakon zanga-zangar da matasa ke yi akan dakatar da SARS

- Daya daga cikin al'amarin da yayi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani na zaluncin da 'yan sanda ke yi shi ne yadda suka zalunci wata tsohuwa

- Tsohuwar ta je ofishin 'yan sanda ne don sanin halin da danta, Femi kuti yake, daya daga cikin 'yan sandan ya daga hannu ya sharara mata mari

Al'amura marasa dadi sun yi ta faruwa sakamakon zanga-zangar da matasan Najeriya ke yi akan dakatar da SARS.

Daya daga ciki shine irin zaluncin da aka yi wa wata tsohuwa, wadda uwa ce wurin manajan Singer Oxlade.

Kamar yadda rahotanni suka yi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, hazikin manajan mai suna Ojah Bee na daya daga cikin 'yan zanga-zangar lumana wanda 'yan sanda suka kama a wuraren Surulere a jihar Legas.

A lokacin da tsohuwar, mai tarin shekaru taje ofishin 'yan sanda don sanin halin da danta yake ciki, daya daga cikin 'yan sandan ya daga hannu ya sharara mata mari.

KU KARANTA: Bidiyo da hotunan budurwa ta garzaya wurin aikin saurayinta cikin shigar amare, ta bukaci a daura musu aure

EndSARS: Bidiyon dan sanda yana zazzabga wa tsohuwa mari a wurin zanga-zanga
EndSARS: Bidiyon dan sanda yana zazzabga wa tsohuwa mari a wurin zanga-zanga. Hoto daga @toluuo
Asali: Twitter

KU KARANTA: Majalisar jihar Edo ta yi sabon kakaki, ta dakatar da tsohon kakakin

A wani labari na daban, anyi wani kwarya-kwaryan rikici a majalisar jihar Edo, inda cikin 'yan majalisu 10, 9 suka hada karfi da karfe wurin tube kakakin majalisar, Hon Frank Okiye, sakamakon zargin shi da ake yi da barnar dukiyar al'umma.

Bayan sun tube shi, take-yanke suka zabi wani sabon kakakin majalisar mai suna Hon. Marcus Onobun, wanda ke wakiltar mazabar Esan ta kudu.

Bayan an rantsar dashi take ya rushe duk wata kwamiti sannan ya soke duk wasu nade-nade da tsohon kakakin yayi, inda ya samar da wata kwamitin mutane 3 da zasu kula da shige da ficen kudi a majalisar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel