Mahaifi ya dauka dansa aikin gadi a kamfaninsa, hakan ya janyo cece-kuce

Mahaifi ya dauka dansa aikin gadi a kamfaninsa, hakan ya janyo cece-kuce

- Wani mutum dan Najeriya ya bayyana yadda yake horar da dansa a harkar sana'arsa

- Kamar yadda Felix ya wallafa hoton, yaron nasa sanye da kayan masu gadi a wurin aikin nasa

- Felix ya dauki yaronsa aiki a matsayin maigadi a kamfaninsa, don ya koya masa aikin gadi

Wani mutum dan Najeriya, shugaban kamfanin tsaro na Fionet, yace , don ya koya wa dansa, Uyiogosa makamar sana'a da kuma zama masa uba nagari, ya daukesa aiki a kamfaninsa.

Yayin da yayi wallafarsa a LinkedIn, ya wallafa hoton dansa sanye da kayan masu gadi.

A yadda ya wallafa, ya jefa wa iyaye tambaya, akan idan zasu iya koyawa yaransu sana'arsu ko kuma zasu barsu hakanan kada su wahala?

Felix ya godewa Ubangiji da ya bashi damar taso da yaronsa cikin tarbiyya don su zama 'ya'yan da zasu jagoranci al'umma.

Wallafar tasa ta janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani, inda wasu ke cewa ya burgesu da salon tarbiyyantar da yaronsa.

Wani Bala ya ce: "Felix gaskiya na dade ban ga mahaifin da ya birgeni kamar ka ba. A zamanin nan, taso da yara cikin irin wannan yanayin yana da matukar wahala."

Kelechi Uchenna yace: "Nidai zan nuna wa 'ya'yana yanayin sana'a ta, idan suna son sana'ar zanyi farin ciki, idan basaso kuma, su je su yi tasu sana'ar."

KU KARANTA: Kotu ta yanke wa gagarumin makashin jama'a hukuncin kisa a Delta

Mahaifi ya dauka dansa aikin gadi a kamfaninsa, hakan ya janyo cece-kuce
Mahaifi ya dauka dansa aikin gadi a kamfaninsa, hakan ya janyo cece-kuce. Hoto daga LinkedIn/Felix
Asali: UGC

KU KARANTA: EndSARS: Fadar shugaban kasa ta bayyana abinda take yi a kan zanga-zanga

A wani labari na daban, hankula sun karkata akan bidiyon wata mata da tayi shiga irin ta amare a Los Vegas. A gefenta akwai kawayenta wadanda suka yi ado da wasu suturu masu kalar ruwan kasa, da takalma masu tsayi.

Matar, wadda ba'a bayyana sunanta ba ta matsa cewa sai ta ga saurayinta dake aiki a wani shago. Tare da matar akwai Fasto, kuma tana rike da zoben daurin aure. Matar bata bukatar jin kalmar "a'a" daga bakin saurayin nata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel