Bidiyon saurayi yana hana budurwa satar ruwan lemunsa a wurin cin abinci

Bidiyon saurayi yana hana budurwa satar ruwan lemunsa a wurin cin abinci

- Wani bidiyo mai ban dariya ya karade shafukan sada zumuntar zamani, wanda wani mawaki, Daniel Marven ya wallafa

- A bidiyon, an ga inda wata budurwa ta fakaici idon saurayin ta, ta juyar da kofin lemun da saurayinta yake sha

- Saurayin bai yi kasa a guiwa ba, inda yayi hanzarin kwace kofin lemun nasa daga hannun budurwar tasa

Wani bidiyo mai ban dariya na wata budurwa da saurayinta a wurin cin abinci ya karade shafukan sada zumuntar zamani.

Inda maza da dama suka yi ta yaba wa jarumtar saurayin.

A Bidiyon, an ga yadda saurayin ke kokarin kwace lemunsa daga hannun budurwarsa dake jin kishi.

A Bidiyon da wani mawaki, Daniel Marven ya wallafa, an ga saurayi da budurwarsa zaune suna soyayyarsu a wani wurin cin abinci.

Ba'ayi nisa cikin Bidiyon ba sai budurwarsa ta fakaici idonsa ta dauki kofin lemunsa za ta sata ta sha.

Saurayin yayi hanzarin amshe kofin nasa daga hannunta, inda yake ja mata kunne akan kada ta kuskura ta sha masa lemunsa, sai dai taje ta siyo nata.

Ba saurayin ne kadai baya son budurwarsa ta ci masa abinci ko abin sha ba, akwai samari da dama da suka tsani hakan, kawai babu yadda suka iya ne yasa suke barin 'yan matan nasu.

KU KARANTA: Sunaye da ma'aikatu: Ganduje ya sauya wa manyan sakatarori 8 wurin aiki, ya nada 4 sabbi

Bidiyon saurayi yana hana budurwa satar ruwan lemunsa a wurin cin abinci
Bidiyon saurayi yana hana budurwa satar ruwan lemunsa a wurin cin abinci. Hoto daga @danielmaven
Asali: UGC

KU KARANTA: EndSARS: Fadar shugaban kasa ta bayyana abinda take yi a kan zanga-zanga

A wani labari na daban, babbar Kotun dake zama a Fatakwal, jihar Ribas ta yanke wa wani makashi, Gracious David-West, hukuncin kisa ta hanyar rataya, sakamakon kashe mata 9 a Otal daban-daban da yayi a jihohin Najeriya.

David-West, cikakken dan jihar Ribas, ya kashe mata 9, tsakanin watan Yuli da Satumbar 2019, sannan ya kai wa mace ta 10 hari, mai suna Benita Etim hari, amma bai samu nasara ba, hakan ya jawo tonuwar asirinsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel