Yadda uwargida ta hargitsa taron bikin mijinta da wata budurwa (Bidiyo)

Yadda uwargida ta hargitsa taron bikin mijinta da wata budurwa (Bidiyo)

- Bidiyon wata mata da ta hargitsa wani aure ya karade shafin sada zumuntar zamani na Instagram

- An ga inda wata mata goye da jariri a bayanta ta bayyana a wurin daurin aure, inda ta fallasa sirrin angon

- Matar tayi ikirarin cewa Angon mijinta ne, kuma yanzu haka suna da yara kuma suna zaune lafiya da juna

Mediagist sun wallafa wani bidiyo a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram, wanda yake nuna wata mata da ta hargitsa wani aure, inda tayi ikirarin cewa ita matar angon ce.

Ranar farin cikin wata Amarya ta koma ranar da tafi kowacce rana bakin ciki da takaici a rayuwarta.

An ga wata mata ta bayyana ta fallasa boyayyen sirrin Angon, inda tayi ikirarin cewa mijinta ne shi har suna da 'ya'ya biyu.

Matar ta bayyana a wurin daurin auren da yaro goye a bayanta. Tace lallai har yanzu akwai igiyar aurensa a kanta, kuma suna nan tare cikin soyayya.

Ta kara da cewa, bata ga dalilin da zai sa ya kara aure ba, tunda yanzu haka suna da yara tare har biyu.

Yadda uwargida ta hargitsa taron bikin mijinta da wata budurwa (Bidiyo)
Yadda uwargida ta hargitsa taron bikin mijinta da wata budurwa (Bidiyo). Hoto daga @mediagist/Instagram
Asali: Instagram

KU KARANTA: COVID-19: An soke biyan kudin makaranta a dukkan makarantun Abuja

A wani labari na daban, hankula sun karkata akan bidiyon wata mata da tayi shiga irin ta amare a Los Vegas. A gefenta akwai kawayenta wadanda suka yi ado da wasu suturu masu kalar ruwan kasa, da takalma masu tsayi.

Matar, wadda ba'a bayyana sunanta ba ta matsa cewa sai ta ga saurayinta dake aiki a wani shago. Tare da matar akwai Fasto, kuma tana rike da zoben daurin aure. Matar bata bukatar jin kalmar "a'a" daga bakin saurayin nata.

An nuna matar tana fuskantar saurayin nata, inda tace indai har yaki amincewa da tayin aurenta to tabbas zata rabu dashi.

Matar ta shayar da mutane da dama mamaki, a yadda ta dage kuma da alamun ta gama auna komai.

Saurayin yayi mamakin al'amarin, inda ya daura kansa akan cinyarsa saboda tsananin mamaki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel