Da duminsa: Malamai sun fatattaki daliban makarantun Abuja, sun hana karatu

Da duminsa: Malamai sun fatattaki daliban makarantun Abuja, sun hana karatu

- Dalibai da ke karatu a makarantun babban birnin tarayya Abuja sun koma gidajensu bayan da malaman suka kore su daga azuzuwa

- Malaman sun kori daliban ne sakamakon gaza biyansu albashi mafi karanci na N30,000 da kuma basussukan da suke bi

- Kungiyar NUT reshen FCT ta ce ba za ta koyar da daliban makarantun firamare na Abuja ba, har sai an kaddamar mafi karancin albashi ga malaman

Labarin da ke shigo mana yanzu na nuni da cewa dalibai da ke karatu a makarantun babban birnin tarayya Abuja sun koma gidajensu bayan da malaman suka kore su daga azuzuwa.

A ranar litinin ne dai aka bude makarantu a babban birnin tarayya Abuja don ci gaba da karatu, tun bayan shafe hutun watanni bakwai sakamakon barkewar annobar COVID-19.

Malaman karkashin kungiyar NUT reshen Abuja sun ce shugaban karamar hukumar birnin tarayyar ya gaza kaddamar da albashin N30,000 ga malaman da kuma biyan basussuka.

KARANTA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe basarake Alhaji Musa Abubakar a gidansa

Da duminsa: Malamai sun fatattaki daliban makarantun Abuja, sun hana karatu
Da duminsa: Malamai sun fatattaki daliban makarantun Abuja, sun hana karatu @vanguardngrnews
Asali: UGC

A yayin da wakilin jaridar Vanguard ya ziyarci makarantar LEA firamare ta Kubwa, wacce ke hade da karamar sakandire, malamai sun kori daliban ne tun wajen karfe 8 na safiya.

Daliban sashen karamar sakandire ne kawai aka bari suna karatu sakamakon malaman da ke koyar da su sun samu karin albashin daga gwamnatin babban birnin tarayyar.

A cikin watan Satumba, shugaban kungiyar, Stephen Knabayi ya umurci mambobin kungiyar da su bijirewa aiki idan an bude makarantu.

KARANTA WANNAN: Diyar Atiku Abubakar ta bayyana wanda za ta goyi baya ya shugabanci kasa 2023

Ya ce a yayin da gwamnatin FCT ta fara biyan mafi karancin albashi na N30,000, ba a waiwayi malaman da ke koyarwa a makarantun firamare nakananan hukumomi 6 na birnin tarayyar ba.

A ranar 8 ga watan Oktoba, FCTA ta sanar da bude makarantu a ranar Litinin 12 ga watan Oktoba, inda ta sanar da soke zango na uku na karatun makarantu.

Haka zalika gwamnatin babban birnin tarayyar ta gargadi makarantu masu zaman kansu da su kauracewa karbar kudaden makaranta na wannan zangon da aka soke.

Ministan Abuja, Malam Muhammad Musa Bello wanda ya bayar da wannan umurnin a taron masu ruwa da tsaki a Abuja, ya sanar da cewa za a bude makarantun kwana a ranar Lahadi.

A wani labarin, Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton an dauko hayarsu don aikata kisa sun kashe Alhaji Musa Abubakar, Dagachin kauyen Runji da ke mazabar Auchan a karamar hukumar Ikara, jihar Kaduna.

'Yan ta'addar sun kashe Basaraken ne da duku-dukun safiyar ranar Lahadi bayan sun kutsa kai zuwa cikin gidansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel