Bayan kwasar gara, mutum daya ya mutu yayin da 6 ke kwance rai a hannun Allah

Bayan kwasar gara, mutum daya ya mutu yayin da 6 ke kwance rai a hannun Allah

- 'Yan sanda sun balla kofar wani gida a Benin, inda suka riski mutanen gidan a mawuyacin hali

- Sun samu 1 daga cikin mutanen gidan a mace, 6 kuma anyi gaggawar tafiya da su asibiti

- 'Yan sandan sunyi ta hasashen abinda ya faru dasu, inda suke zargin ko abinci mai guba suka ci

'Yan sanda sun balle kofar wani gida a Benin inda suka riski mutane 7 a mawuyacin hali. Mutum 1 daga cikinsu ya rasu, 6 kuma suna asibiti.

Ana zargin sun ci abinci sai suka kwanta, basu tashi washegari ba. Wani dan sanda ya sanar da jaridar Daily Trust cewa watakil hayakin janareto da suka kunna ne ya jawo wannan matsalar.

Al'amarin ya faru ne a gida mai lamba 40 akan titin Otete, kusa da layin masaka a Ogida quarters a cikin Benin City.

A lokacin da manema labarai suka isa wurin, basu tarar da mutane da yawa ba a wajen gidan. Makwabta sun yi ta tunanin ko sun ci lalataccen abinci ne.

Wata makwabciyarsu mai suna Rachel Anyanwa tace, "Kwana 5 kenan da matar mutumin ta rasu.

"Wadanda aka kai asibiti yaransa ne da 'yan uwansa da suka zo yi masa ta'aziyyar mutuwar matar sa."

Wata makwabciyarsu, Christy Igbinadilor, ta ce basu san faruwar lamarin ba sai da wani mutum yazo tambayarta akan abinda ke faruwa da makwabtanta.

A yadda tace, mutumin da yazo wurinta, yace 'ya'yan mai gidan ne yayi ta kiran shi daga Fatakwal yace ya zo yaji dalilin da baya ansa kiransa.

Sai taba mutumin shawarar kwankwasa musu kofa, idan yaji shiru yaje ya sanar da 'yan sanda.

Tace sai bayan 'yan sandan sun zo ne suka balla kofar, inda suka riski mutanen gidan a mawuyacin hali, aka tafi da su asibiti.

KU KARANTA: Bidiyon sallar Juma'a ta farko ta Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli

Bayan kwasar gara, mutum daya ya mutu yayin da 6 ke kwance rai a hannun Allah
Bayan kwasar gara, mutum daya ya mutu yayin da 6 ke kwance rai a hannun Allah. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Rundunar soji ta salwantar da ran wani shugaban 'yan bindiga a Filato

A wani labari na daban, daga watan Janairu zuwa yanzu, akalla mutane 36 sun mutu, 470 sun rasa gidajensu sakamakon ambaliyar ruwan sama a jihar Sokoto.

Mustapha Umar, shugaban hukumar wayar da kai da rage radadi ta jihar Sokoto (SEMA) ya bayyanar da hakan a wani taro na masu ruwa da tsaki a harkar ibtila'i a ranar Alhamis a jihar Sokoto.

Umar yace , kusan hectares 302 zuwa 500 na gonaki sun hade wuri guda, kuma dabbobi akalla 120 ne suka mutu sakamakon ambaliyar a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel