EndSARS: Fadar shugaban kasa ta bayyana abinda take yi a kan zanga-zanga

EndSARS: Fadar shugaban kasa ta bayyana abinda take yi a kan zanga-zanga

- Hadimin shugaban kasa na harkar watsa labarai, Bashir Ahmad, yace an sanar da shugaban kasa zalincin da 'yan sandan SARS ke yi

- Yace shugaban kasar ya tattauna da IG din 'yan sanda akan al'amarin, kuma ya tabbata za'a dauki matakin da ya dace

- Yace 'yan Najeriya suna da damar bayyana damuwarsu akan zalinci ko mungunta ta hanyoyin da suka dace don hakkinsu ne yin hakan

Fadar shugaban kasa tace an sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari akan zanga-zangar da matasa ke yi saboda kashe-kashen da jami'an SARS ke yi.

Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa akan harkokin watsa labarai ya sanar da hakan a ranar Juma'a, 9 ga watan Oktoba, matasa na tsaka da zanga-zanga akan kisan wulakanci da 'yan sanda ke yi.

Yace Sifeta janar na 'yan sanda, Muhammed Adamu ya sanar da shugaban kasar a ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoba.

Ahmed yace shugaban kasa zai tabbatar ya dauki mataki akai, kuma zai sauyasu da wasu 'yan sandan, yadda zai faranta wa 'yan Najeriya.

Hadimin Buharin ya ce 'yan Najeriya suna da damar bayyanar da damuwarsu idan har shugabanninsu sun yi ba daidai ba.

Kamar yadda yace, "Mutanen kirkin Najeriya suna da damar yin zanga-zanga saboda rashin tausayin da 'yan sanda ke nuna musu, ko kuma wani abu da sukaga bai yi musu ba."

Ya kara da cewa, "Shugaban kasa ya tattauna matsalar da IG na 'yan sanda, don haka na tabbatar za'a dauki mataki akai."

KU KARANTA: Magidanci mai 'ya'ya 19 ya sanya wa autansa suna 'Ya Isa Haka' (Hotuna)

EndSARS: Fadar shugaban kasa ta bayyana abinda take yi a kan zanga-zanga
EndSARS: Fadar shugaban kasa ta bayyana abinda take yi a kan zanga-zanga. Hoto daga @BashirAhmad
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rundunar soji ta salwantar da ran wani shugaban 'yan bindiga a Filato

A wani labari na daban, daga watan Janairu zuwa yanzu, akalla mutane 36 sun mutu, 470 sun rasa gidajensu sakamakon ambaliyar ruwan sama a jihar Sokoto.

Mustapha Umar, shugaban hukumar wayar da kai da rage radadi ta jihar Sokoto (SEMA) ya bayyanar da hakan a wani taro na masu ruwa da tsaki a harkar ibtila'i a ranar Alhamis a jihar Sokoto.

Umar yace , kusan hectares 302 zuwa 500 na gonaki sun hade wuri guda, kuma dabbobi akalla 120 ne suka mutu sakamakon ambaliyar a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel