Matar aure ta haifa mace bayan watanni biyar da haihuwar tagwaye

Matar aure ta haifa mace bayan watanni biyar da haihuwar tagwaye

- Wani abin al'ajabi ya faru a jihar Legas, wanda wata mata bayan haihuwar tagwaye da watanni 5, ta haifi santaleliyar jaririya

- Bayan haihuwar tagwaye a watan Afirilun 2020, sai ta fara fuskantar matsanancin ciwon cikin, likitoci sun duba amma basu ga komai ba

- Bayan neman taimakon wata mai maganin gargajiya, ta kara zuwa likitoci suka duba ta, inda suka tabbatar da cikin, kuma ta haifeshi a watan Satumba 2020

Wani abin al'ajabi ya faru a jihar Legas, wata mata ta kara haihuwa bayan watanni 5 da haihuwar tagwaye.

Kamar yadda Enate Ogedegbe ya wallafa bikin sunan jariran a ranar Lahadi, 4 ga watan Oktoba, tare da wani Fasto Daniel Osierih, ya ce sai da matar tayi shekaru 7 da aure kafin ta samu haihuwar.

Shekaru 4 da suka wuce, matar ta haifi tagwaye. A watan Afirilun 2020, ta kara haihuwar 'yan biyu, daga nan ne ta fara jin wani ciwon ciki.

Da likitoci suka auna ta, basu ga komai ba. Bayan watanni 3 da haihuwar tagwaye, sai aka kara aunata inda aka gano tana da wani cikin.

A ranar 18 ga watan Satumban 2020, bayan watanni 5 kenan da haifar tagwayen, sai ta haifi santaleliyar jaririya.

Kamar yadda ya wallafa: "Ni da Fasto Daniel Osierih, mun samu damar halartar wannan radin sunan. Shekaru 7 kenan da ma'auratannan suka yi aure, Ubangiji ya azurta su da tagwaye wadanda yanzu haka shekarunsu 4.

"Sai ga wasu tagwayen a watan Afirilu 2020. Bayannan ne uwar ta fara fama da wani matsanancin ciwon ciki, likitoci sun auna ta amma basu ga komai ba."

Har ta fara zuwa wurin wata mata mai maganin gargajiya tana shafa mata magani a cikin.

Dama mijinta bayanan lokacin kullen nan, sai makon da ya wuce ya dawo Najeriya.

KU KARANTA: Kotu ta raba auren shekara 7 a kan rashin biyan kudin makaranta

Matar aure ta haifa mace bayan watanni biyar da haihuwar tagwaye
Matar aure ta haifa mace bayan watanni biyar da haihuwar tagwaye. Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Akwai yuwuwar maza masu babbar murya su fi sauran maza iya cin amana - Sabon bincike

A wani labari na daban, a ranar Alhamis, rundunar OPSH ta samu nasarar kashe shugaban 'yan bindiga dake kauyen Tafawa a karamar hukumar Barikin Ladi a jihar Plateau, Daily Trust ta wallafa.

Manjo Janar John Enenche, kakakin rundunar soji, ya sanar da hakan a wata takarda, inda ya sanar da ragargazar 'yan ta'adda da suka samu nasarar yi.

"A 'yan kwanakin nan, rundunar soji sun samu nasarori sakamakon amfani da dabaru masu dumbin yawa wurin ragargazar 'yan ta'adda." yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel