COVID-19: An soke biyan kudin makaranta a dukkan makarantun Abuja

COVID-19: An soke biyan kudin makaranta a dukkan makarantun Abuja

- Ministan Birnin tarayya, Muhammad Musa Bello, ya bada umarnin bude makarantu ranar Litinin, 12 ga watan Oktoba 2020

- Ya bada umarnin ne bayan tuntubar kwamitin shugaban kasa akan COVID-19, inda aka amince da bude makarantun

- Ya kuma gindaya sharudda, wadanda yace dole ne makarantu su kiyaye, rashin kayayesu zai janyo rufe makarantun

Ministan Birnin Tarayya, Muhammad Musa Bello, ya bada umarnin bude makarantu a ranar Litinin, 12 ga watan Oktoba 2020.

Dakta Fatima Abdurrahman, shugabar kwamitin tsara bude makarantu, wadda ministan ya nada bayan barkewar annobar Coronavirus, ta sanar da hakan a tattaunawar da tayi da manema labarai a Abuja.

Ta ce ministan ya umarci makarantu da su soke karatuttukan zango na 3, ya ce su yi wa yara bita akan karatuttukan zango na 2, su kuma yi musu jarabawa akai cikin makonni 2.

Ministan ya gargadi makarantu masu zaman kansu, inda ya ce kada su amshi kudin makarantar zango na 3, kuma su tabbatar da cewa duk girman aji yara basu zarce guda 25 ba.

Ya ce,

Ya kara da cewa, "Dole ne kowacce makaranta ta guji cunkushe yara wuri guda, kuma suyi matukar kokari wurin bin dokokin da gwamnatin tarayya ta gindaya."

Ministan ya tsoratar da makarantu, inda yace duk makarantar da ta saba ka'idoji har cutar coronavirus ta barke, zata fuskanci hukunci, ciki kuwa har da rufe makarantar gaba daya.

Yace sai da aka yi nazari mai yawa, tare da tuntubar kwamitin Shugaban kasa ta COVID-19, tukunna suka amince da bude makarantu a Abuja tare da bin matakan da suka dace.

KU KARANTA: Ambaliyar ruwa: Rayuka 36 sun salwanta, mutum 470 sun rasa gidajensu

COVID-19: An soke biyan kudin makaranta a dukkan makarantun Abuja
COVID-19: An soke biyan kudin makaranta a dukkan makarantun Abuja. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Dakarun soji sama sun ragargaji 'yan bindigar daji a Kaduna

A wani labari na daban, Jami'ar Chongqing da ke China ta dukufa wurin yin wannan nazarin, inda ta bincika maza 116 da mata 145 kuma ta tabbatar da hakan.

Wadanda aka yi nazari a kansu sun kai a kalla shekaru 20 da haihuwa, inda aka yi ta musu tambayoyi akan yanayin dagewa da jajircewarsu a kan soyayya da mace daya.

Kamar yadda aka gano, daga cikin wadanda aka bincika, masu babbar murya sun fi tara 'yanmata da yawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel