Kotu ta yanke wa gagarumin makashin jama'a hukuncin kisa a Delta

Kotu ta yanke wa gagarumin makashin jama'a hukuncin kisa a Delta

- Babbar Kotun dake zama a Fatakwal, jihar Ribas ta yanke wa wani makashi hukuncin kisa ta hanyar rataya

- David-West ya kashe mata 9 a Otal daban-daban a jihohin Najeriya, dubunsa ta cika a lokacin da ya kaiwa mace ta 10 hari

- Bayan hukuncin, lauyan makashin ya nemi sassauci a wurin kotu saboda David-West yana da yara har 3, amma kotu ta ki

Babbar Kotun dake zama a Fatakwal, jihar Ribas ta yanke wa wani makashi, Gracious David-West, hukuncin kisa ta hanyar rataya, sakamakon kashe mata 9 a Otal daban-daban da yayi a jihohin Najeriya.

David-West, cikakken dan jihar Ribas, ya kashe mata 9, tsakanin watan Yuli da Satumbar 2019, sannan ya kai wa mace ta 10 hari, mai suna Benita Etim hari, amma bai samu nasara ba, hakan ya jawo tonuwar asirinsa.

Alkalin da yayi shari'ar, Alkali Adolphus Enebeli, bayan samun gamsassun hujjojin da suka tabbatar da laifukan David-West, ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An sallami Nimi ThankGod, mai kula da daya daga cikin Otal din da aka yi ta kashe matan, sakamakon gano cewa babu hannunta a kashe-kashen, duk da lauyan makashin yaso ya makala mata laifin.

Lauyan David-West, Vincent Chukwu, ya roki kotu tayi sassauci saboda wanda yake karewa uba ne ga yara 3.

Saidai lauyan masu kara, Chidi Ekeh, yace David-West bai cancanci wani sassauci ba, ya roki kotu da ta tabbatar da yiwa mamatan adalci.

A lokacin da makashin yana hannun 'yan sanda a watan Satumba, ya tabbatar da ya kashe mata 7, 1 a jihar Legas, 1 a Owerri, daya a jihar Imo sai 5 a jihar Rivers.

Ekeh ya tabbatar wa manema labarai cewa, za'ayi hukunci bisa adalci don duk masu niyyar yin mummunan aiki irin nasa su shiga taitayinsu.

KU KARANTA: Magidanci mai 'ya'ya 19 ya sanya wa autansa suna 'Ya Isa Haka' (Hotuna)

Kotu ta yanke wa gagarumin makashin jama'a hukuncin kisa a Delta
Kotu ta yanke wa gagarumin makashin jama'a hukuncin kisa a Delta. Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ambaliyar ruwa: Rayuka 36 sun salwanta, mutum 470 sun rasa gidajensu

A wani labari na daban, wata kotu dake zama a Kubwa, Abuja ta tsinke igiyar aure mai shekaru 7, ranara Laraba, tsakanin Salamat Dauda da mijinta, Isiyaka, akan kin biya wa yaransa kudin makaranta.

Salamat ta roki kotu da ta tsinke igiyar aurenta da Isiyaka saboda rashin sauke nauyinsa a matsayin mijinta kuma uban 'ya'yanta.

Alkali mai shari'a, Muhammad Adamu, ya ce matar za ta yi zaman iddah na watanni 3 kafin ta sake wani auren.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel