Magidanci mai 'ya'ya 19 ya sanya wa autansa suna 'Ya Isa Haka' (Hotuna)

Magidanci mai 'ya'ya 19 ya sanya wa autansa suna 'Ya Isa Haka' (Hotuna)

- Wani mutum mai suna Zeher Gezer ya sanya wa dansa na 19 suna Yeter- ma'ana "ya isa haka"

- Yace yanzu haka, ciyar da iyalansa na gagararsa, saboda ya rasa aikinsa da yayi

- Yace da ya san haka za ta kasance, da bai tara mata 2, ya kuma haifi yara 19 ba

Wani mutum mai mata 2 da yara 19 ya sanya wa jaririn da aka haifa masa Yeter - ma'ana "ya isa haka"

Zeher Gezer, wanda yake zaune a garin Diyarbakir a kudu maso gabas ta Turkiyya, ya haifa yara 19 da matansa 2.

Yace shi da matansa na son yaransu, amma gaskiya yanayin rayuwa ya canja. Ga Coronavirus ta dakatar da komai, yanzu haka ayyuka sun yi wahala, ciyar da iyalinsa ya zama babban aiki.

A kasar Turkiyya, auren mace fiye da daya bai halasta ba, saidai idan addini ya amince wa mutum, amma ba za'a yi wa auren rijista ba.

Matan nasa, Dilber da Kraniye Gezer sun yi farinciki da wannan al'amarin, duk da a baya sun ki yarda, sai da suka ga cewa 'yan uwansu ne ke taimaka musu wurin ciyar da gidan.

Matarsa ta farko, Dilber, mahaifiyar yaran guda 10 tace, "Da farko na fara kishi akan karin auren da yayi, amma yanzu har taimakon juna muke yi, ni da amaryarsa.

"Kowa nada yaransa, na dauki yaranta a matsayin nawa, itama haka." Cewar Dilber.

Zeher yace yana iya kokarinsa na ciyar da iyalinsa, amma ya rasa aikinsa sakamakon annobar Coronavirus.

Ya kara da cewa: "Da na san abinda zai faru kenan, da ban tara yara da yawa ba."

Duk da mutane na kokarin taimakon su, amma yaran 19 sukan yi bacci da yunwa.

Magidanci mai 'ya'ya 19 ya sanya wa autansa suna 'Ya Isa Haka' (Hotuna)
Magidanci mai 'ya'ya 19 ya sanya wa autansa suna 'Ya Isa Haka' (Hotuna). Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jama'a sun saki baki wurin kallon akuyar da ke yawo da kafafu biyu

Magidanci mai 'ya'ya 19 ya sanya wa autansa suna 'Ya Isa Haka' (Hotuna)
Magidanci mai 'ya'ya 19 ya sanya wa autansa suna 'Ya Isa Haka' (Hotuna). Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ambaliyar ruwa: Rayuka 36 sun salwanta, mutum 470 sun rasa gidajensu

Magidanci mai 'ya'ya 19 ya sanya wa autansa suna 'Ya Isa Haka' (Hotuna)
Magidanci mai 'ya'ya 19 ya sanya wa autansa suna 'Ya Isa Haka' (Hotuna). Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

A wani labari na daban, wata kotu dake zama a Kubwa, Abuja ta tsinke igiyar aure mai shekaru 7, ranara Laraba, tsakanin Salamat Dauda da mijinta, Isiyaka, akan kin biya wa yaransa kudin makaranta.

Salamat ta roki kotu da ta tsinke igiyar aurenta da Isiyaka saboda rashin sauke nauyinsa a matsayin mijinta kuma uban 'ya'yanta.

Alkali mai shari'a, Muhammad Adamu, ya ce matar za ta yi zaman iddah na watanni 3 kafin ta sake wani auren.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel