Ambaliyar ruwa: Rayuka 36 sun salwanta, mutum 470 sun rasa gidajensu

Ambaliyar ruwa: Rayuka 36 sun salwanta, mutum 470 sun rasa gidajensu

- Daga watan Janairu zuwa yanzu, fiye da mutane 36 sun rasa rayukansu a jihar Sokoto sakamakon ambaliyar ruwan sama

- Umar Muhammed, Shugaban SEMA, yace fiye da mutane 470 sun rasa gidajensu, kuma dabbobi 120 sun mutu duk saboda ambaliyar

- Yace a cikin kananan hukumomi 23 na jihar Sokoto, 19 sun fuskanci wannan ibtila'i sakamakon ruwan saman shekarar 2020

Daga watan Janairu zuwa yanzu, akalla mutane 36 sun mutu, 470 sun rasa gidajensu sakamakon ambaliyar ruwan sama a jihar Sokoto.

Mustapha Umar, shugaban hukumar wayar da kai da rage radadi ta jihar Sokoto (SEMA) ya bayyanar da hakan a wani taro na masu ruwa da tsaki a harkar ibtila'i a ranar Alhamis a jihar Sokoto.

Umar yace , kusan hectares 302 zuwa 500 na gonaki sun hade wuri guda, kuma dabbobi akalla 120 ne suka mutu sakamakon ambaliyar a jihar.

Yace ambaliyar ruwan shekarar 2020 ta shafi kananan hukumomi 19 a cikin 23 na jihar Sokoto.

Dr Kofoworola Soleye, shugaban NEMA ya wakilci Darekta janar AVM Muhammadu Muhammed a wurin taron da aka yi don tattaunawa akan samar da mafita ga mutanen jihar Sokoto.

Muhammed yace masu ruwa da tsaki zasu samar da hanyoyin da mafita kamar yadda aka yi a shekarun baya.

A cewarsa, zaman zai taimaka wurin samar da hanyoyin da za'ayi don kawo karshen wannan musiba a jihar Sokoto.

A cewarsa, "ya kamata NEMA ta hada karfi da karfe da wasu cibiyoyin don samun yadda za'a bullo wa duk wata annoba data kunno kai, kamar yadda aka yi na COVID-19 da ta addabi duniya.

"Yakamata wannan shirin ya kawo mafita da hanyoyin da za'a bi don magance duk wata annoba da ta kunno kai."

Muhammed yace NEMA na bukatar tsari da kuma gudanarwa ta musamman, don ganin karshen duk wata musiba da ta iso jihar.

Ya kara da cewa, ba NEMA kadai ba, kowanne dan Najeriya yana da alhakin jajircewa da dagewa wurin bada gudunmawa daidai gwargwado don ganin an cimma gaci.

KU KARANTA: Kotu ta raba auren shekara 7 a kan rashin biyan kudin makaranta

Ambaliyar ruwa: Rayuka 36 sun salwanta, mutum 470 sun rasa gidajensu
Ambaliyar ruwa: Rayuka 36 sun salwanta, mutum 470 sun rasa gidajensu. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Akwai yuwuwar maza masu babbar murya su fi sauran maza iya cin amana - Sabon bincike

A wani labari na daban, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bai wa gwamnatin tarayya shawarar rage cin bashi da kuma samar da hanyoyin samun kudin shiga.

Lawan yayi maganar ne bayan an gabatar da kiyasin kididdigar kudin da za'a kashe tsakanin 2021 a ranar Alhamis.

Ya ce: "Ya kamata mu dage wurin tabbatar da hanyoyin samun kudin shiga sun inganta. Ya kamata mu dage wurin toshe duk wani gurbi. Akwai ayyukan da ba dole sai an aro kudi za'ayi su ba."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel