So suke su salwantar da rai na kamar yadda suka yi wa Bola Ige - Fayose ya koka

So suke su salwantar da rai na kamar yadda suka yi wa Bola Ige - Fayose ya koka

- Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Gwamna Ayo Fayose yace wasu 'yan ta'addan jam'iyyar PDP suna kokarin kashe shi

- 'Yan ta'addan sun tare shi a hanyarsa na zuwa kamfen din PDP na gwamnan jihar Ondo har suna cire mishi hula

- Yace ba zai kyale wannan al'amarin ba, sai ya kai kararsu wajen cibiyoyin tsaro an gano su kuma an hukunta su

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Gwamna Ayo Fayose yace wasu 'yan ta'addan jam'iyyar PDP na yankin kudu maso yamma na yunkurin kashe shi, kamar yadda suka kashe tsohon Antony Janar kuma minstan shari'a, Chief Bola Ige.

Fayose yayi korafin ne sakamakon cire masa hula da wasu 'yan ta'adda suka yi a hanyarsa ta zuwa wani taron kamfen na gwamnan jihar Ondo a karkashin jam'iyyar PDP ranar Laraba.

Dama sai da aka cire hular Ige a fadar Ooni na Ife da awanni kadan kafin a kasheshi a gidansa da ke Bodija a jihar Ibadan ranar 23 ga watan Dismba 2001.

Fayose yace zai dauki matakin da ya dace akan wannan yunkurin kisar da aka yi mishi, zai tabbatar ya gabatar da korafinsa ga cibiyoyin tsaro da kuma hukumomin dake tafiyar da al'amarin jam'iyyar don daukar matakin da ya dace.

Yace wajibi ne cibiyoyin tsaro su dage wurin gano wadanda suke da alhakin daukar nauyin wadannan 'yan ta'adda.

Yace, "Haka suka cire wa Chief Bola Ige hula a Ile-Ife, jihar Osun, kuma munsan abinda ya biyo baya. Don haka bazan kyale wannan ba, wajibi ne in dauki mataki."

Ya kara da cewa, "Tabbas shirya wannan al'amarin aka yi don har sun fara yada bidiyon abinda suka aikata min."

"Don haka ba kuskure bane, shirya shi aka yi. Amma duk wandanda keda hannu akai, sunyi shashanci, saboda Ayo Fayose, Osokomole ba wawa bane," cewarsa.

"Daga ganin wannan wautar, sabon shigar jam'iyyar PDP ne, basu damu da bata sunan jam'iyya ba in dai za su samu nasara akan abinda suke shiryawa."

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan majalisar nadin sarakuna 5 sun yi wa Bamalli mubaya'a

So suke su salwantar da rai na kamar yadda suka yi wa Bola Ige - Fayose ya koka
So suke su salwantar da rai na kamar yadda suka yi wa Bola Ige - Fayose ya koka. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

KU KARANTA: Matar aure ta wallafa sunan mijinta a kafar sada zumunta a kan karya da yayi mata ya tare da karuwa a otal

A wani labari na daban, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bai wa gwamnatin tarayya shawarar rage cin bashi da kuma samar da hanyoyin samun kudin shiga.

Lawan yayi maganar ne bayan an gabatar da kiyasin kididdigar kudin da za'a kashe tsakanin 2021 a ranar Alhamis.

Ya ce: "Ya kamata mu dage wurin tabbatar da hanyoyin samun kudin shiga sun inganta. Ya kamata mu dage wurin toshe duk wani gurbi. Akwai ayyukan da ba dole sai an aro kudi za'ayi su ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel