Akwai yuwuwar maza masu babbar murya su fi sauran maza iya cin amana - Sabon bincike

Akwai yuwuwar maza masu babbar murya su fi sauran maza iya cin amana - Sabon bincike

- Bincike ya nuna cewa maza masu babbar murya sun fi cin amana a soyayya

- Jami'ar Chongqing dake China ta bincika maza 116 da mata 145 kuma sun tabbatar da hakan

- Maza masu alamar mazantaka tattare da su sunfi daukar hankalin mata da dama

Kamar yadda bincike ya nuna, maza masu babbar murya sun fi cin amana a soyayya.

Jami'ar Chongqing da ke China ta dukufa wurin yin wannan nazarin, inda ta bincika maza 116 da mata 145 kuma ta tabbatar da hakan.

Wadanda aka yi nazari a kansu sun kai a kalla shekaru 20 da haihuwa, inda aka yi ta musu tambayoyi akan yanayin dagewa da jajircewarsu a kan soyayya da mace daya.

Kamar yadda aka gano, daga cikin wadanda aka bincika, masu babbar murya sun fi tara 'yanmata da yawa.

Binciken ya nuna cewa, maza masu mazantaka sun fi iya yaudara a soyayya akan mazan da suke yanayi da mata.

Hakan yana da jibi da wani sinadarin da garkuwarsu ke saki ma suna 'Testosterone' wanda ke fitar wa jikinsu duk wasu alamu na mazantaka, kama daga murya, gemu, sha'awarsu ga mata da sauran su.

Binciken ya nuna cewa, maza masu babbar murya suna daukar hankalin mata da dama, wannan dalilin ke sa mata su dinga binsu.

Sannan kuma yanayin maza, tsayi, da kuma muryarsu mai girma na sa mata su dinga rikicewa dominsu.

Idan mazan suka lura da yadda suke burge mata dama, hakan zai hana su tsayawa akan mace daya.

KU KARANTA: Hotunan yadda aka tsananta tsaro a fadar sabon Sarkin Zazzau

Akwai yuwuwar maza masu babbar murya su fi sauran maza iya cin amana - Sabon bincike
Akwai yuwuwar maza masu babbar murya su fi sauran maza iya cin amana - Sabon bincike. Hoto daga Linda Ikeji Blog
Asali: UGC

KU KARANTA: Matar aure ta wallafa sunan mijinta a kafar sada zumunta a kan karya da yayi mata ya tare da karuwa a otal

A wani labari na daban, wata hira tsakanin saurayi da budurwa a kafar sada zumuntar zamani ta WhatsApp tayi ta yawo a yanar gizo. Saurayin, mai suna Stephen da budurwarsa sunyi hira ne akan shirin auren yayarta.

Bayan yayi ta tambayar budurwar ko za ta aureshi na tsawon shekaru 2 amma ta murje ido ta ki. Saurayin bayan ya ga cewa kullum tsufa yake yi, ya nuna lallai ya kosa yayi aure, sai ya sauya akalarsa zuwa yayarta.

A yadda saurayin yace, tunda budurwarsa mai shekaru 24 bata shirya ba, ya tabbatar yayarta mai shekaru 29 a shirye take tayi aure.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel