Ahmed Lawan ya shawarci Buhari da ya guji cin bashi don aiwatar da manyan ayyuka

Ahmed Lawan ya shawarci Buhari da ya guji cin bashi don aiwatar da manyan ayyuka

- Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bai wa gwamnatin tarayya shawarar rage cin bashi

- Yace akwai ma'aikatu da 'yan kasuwa da dama da za'a iya neman kudin shiga daga su, a jarraba yin hakan

- Ya kara da cewa akwai ma'aikatun da aka kirkira kuma kudi na tafiya akan su ko yaushe, a dakatar da hakan

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bai wa gwamnatin tarayya shawarar rage cin bashi da kuma samar da hanyoyin samun kudin shiga.

Lawan yayi maganar ne bayan an gabatar da kiyasin kididdigar kudin da za'a kashe tsakanin 2021 a ranar Alhamis.

Ya ce: "Ya kamata mu dage wurin tabbatar da hanyoyin samun kudin shiga sun inganta. Ya kamata mu dage wurin toshe duk wani gurbi. Akwai ayyukan da ba dole sai an aro kudi za'ayi su ba.

"Muyi kokari wurin gano hanyoyin samun kudi, kamar BOT, kasuwanci tsakanin gwamnati da manyan 'yan kasuwa da sauransu. Gaskiya ya kamata mu rage cin bashi.

KU KARANTA: Operation Kashe Mugu: NAF ta kaddamar da sabon shirin kawar da 'yan bindiga a Arewa

Ahmed Lawan ya shawarci Buhari da ya guji cin bashi don aiwatar da manyan ayyuka
Ahmed Lawan ya shawarci Buhari da ya guji cin bashi don aiwatar da manyan ayyuka. Hoto daga @Dailynigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Iyalai 12,000 za su amfana da tallafin tsabar kudi a jihar Kano

"Akwai 'yan kasuwa da dama da suke da ra'ayin bunkasa ma'aikatunmu, mu basu dama. Muna da cibiyoyi da dama da muka kirkira saboda wata matsala, mu tuntunbi wadannan cibiyoyin idan bukatar haka ta taso.

"Akwai ma'aikatun da ba na dole bane, mun kirkiresu haka nan kuma kullum kudade na shiga, bama wani amfana da su.

"Duk da na san abubuwan da nake fadi suna da wahalar yi, amma ya kamata mu gwada, duk da wasu zasu rasa ayyukan yi amma wajibi ne mu yi abinda ya dace," cewar Lawan.

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya sabon Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, murnar samun sarautar Zazzau.

Shugaban kasar ya kara da shawartarsa da ya zama shugaba ga kowa da kowa. Kamar yadda Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar, ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce wannan lokaci ne mai cike da kalubale.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel