A karon farko, tsohuwar matar Fani Kayode ta magantu a kan mutuwar aurensu

A karon farko, tsohuwar matar Fani Kayode ta magantu a kan mutuwar aurensu

- Precious Chikwendu ta tabbatar wa da duniya mutuwar aurenta da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode

- Bayan ta wallafa hotunan kyawawan yaranta, ta tabbatar wa wani mabiyin ta na Instagram mutuwar auren

- Ta tabbatar masa da cewa lallai aurenta da Fani-Kayode ba lalacewa yayi ba, karewa yayi gaba daya

Precious Chikwendu, ta tabbatar da mutuwar aurenta da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayide.

Matar mai yara 4, ta sanar da mutuwar auren nata bayan ta wallafa hotunan yaranta a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram.

Wani mabiyin ta na Instagram yayi tsokaci a karkashin hoton da ta wallafa, "Aurenki na lalacewa, amma wadannan yaran naki basu saka miki karfin guiwar komawa garesu ba. Na tausaya miki."

Bayan ta ga wannan tsokacin nasa, sai ta mayar masa da martani, inda ta tabbatar mishi da mutuwar auren nata.

Precious ta ce, "Ka lura, karewa aurena yayi, ba lalacewa ba."

KU KARANTA: Operation Kashe Mugu: NAF ta kaddamar da sabon shirin kawar da 'yan bindiga a Arewa

A karon farko, tsohuwar matar Fani Kayode ta magantu a kan mutuwar aurensu
A karon farko, tsohuwar matar Fani Kayode ta magantu a kan mutuwar aurensu. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon murnar da ta barke a Zaria bayan nada Bamalli a sabon Sarki

A wani labari na daban, wani bakanike, Olumayowa Afolabi ya roki kotun Ile-Tuntun dake Ibadan ranar Talata da ta tsinke igiyar aurensa na shekara 17 da matarsa, sakamakon rashin daraja sa da kuma yunkurin kashe shi.

Mutumin mazaunin layin Odeyan-Akanran a Ibadan ya sanar da kotun yadda ya gaji da zama da matarsa saboda marinsa da ta ke yi akai-akai.

"Mai girma mai shari'a, idan da wani zai fada min cewa Mojisola zata dinga dukana, da na karyata shi.

"Ta fara mari na ne a 2018 lokacin akan nayi mata magana akan dambe da tayi da wasu malamai 4 dake zama a gidanmu. Tun daga lokacin tana mari na duk sanda muka samu matsala.

"Sakamakon sabawa da tayi da mari na, tana yi har a gaban kanninta, wanda su da kansu sun sha ja mata kunne akai.

"Wanda yafi kona min rai shine yadda ta yi min tsirara ta kuma zaneni a watan Mayu, saboda na hana ta fita amsar wayarta da daddare.

"Ta riga ta nuna min karara cewa ta daina so na, kuma bata bukatar zama dani," cewar Olumayowa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel