Da duminsa: Buhari ya taya Bamalli murna, ya mika muhimmiyar shawara garesa

Da duminsa: Buhari ya taya Bamalli murna, ya mika muhimmiyar shawara garesa

- Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya taya Ambasada Bamalli murna

- Ya yi kira ga sabon sarkin da yayi amfani da wannan damar wurin hada kan gidajen sarautar

- Ya kara da yi wa sarkin addu'ar hikima da shiriyar Allah ta yadda zai samu sauke nauyin da ke kansa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya sabon Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, murnar samun sarautar Zazzau.

Shugaban kasar ya kara da shawartarsa da ya zama shugaba ga kowa da kowa.

Kamar yadda Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar, ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce wannan lokaci ne mai cike da kalubale.

A don haka yayi kira ga Ambasadan da ya yi amfani da wannan damar wurin hada kan dukkan gidajen sarautar.

"Wannan lokaci ne mai cike da kalubale kuma ina yin amfani da wannan damar wurin kira gareka da ka yi amfani da ita wurin hada kan dukkan gidajen sarautar," Buhari ya shawarci Ambasada Bamalli.

Daga bisani, shugaban kasan ya yi wa sabon Sarkin fatan hikima da kuma shiriyar Allah wurin sauke nauyin da ya hau kansa.

"Ina fatan Allah ya baka hikima da kuma shiriya ta sauke wannan nauyin da ya hau kanka," shugaban kasar ya yi addu'a ga sabon Sarkin.

KU KARANTA: Iyalai 12,000 za su amfana da tallafin tsabar kudi a jihar Kano

Da duminsa: Buhari ya taya Bamalli murna, ya mika muhimmiyar shawara garesa
Da duminsa: Buhari ya taya Bamalli murna, ya mika muhimmiyar shawara garesa. Hoto daga @GovKaduna
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bayan musayar wuta, 'yan Boko Haram sun halaka jami'in JTF a Borno

A wani labari na daban, bayan nadin sabon sarkin Zazzau, an tsananta tsaro a farfajiyar fadar sabon Sarkin Zazzau. Gidan talabijin na Channels sun nuna yadda mutane suka yi ta kutsawa fadar suna murna.

Al'amarin ya biyo bayan nada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19 wanda Gwamna Nasir El-Rufai yayi.

Bamalli ya gaji marigayi sarki Shehu Idris wanda ya rasu a ranar 20 ga watan Satumba, 2020 bayan mulkar masarautar na shekaru 45.

Bamalli ne farkon sarki daga gidan mallawa tun bayan rasuwar kakansa, Sarki Dan Sidi a shekarar 1920. Shekaru 100 kenan da rasuwarsa, sai wannan karon mulki ya dawo gidan mallawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel